Daga Ibraheem El-Tafseer
Rundunar ‘yan sanda a jihar Nasarawar ta ce jami’anta na can suna ƙoƙarin kuɓutar da mai martaba Sarkin Gurku da iyalinsa, waɗanda ‘yan bindiga suka sace.
Rundunar `yan sandan ta tabbatar da cewa da misalin ƙarfe goma na dare, maharan waɗanda ake zargin masu satar mutane ne ɗauke da bindigogi suka kutsa fadar mai martaba Sarkin Gurku, mai daraja ta ɗaya, Alhaji Jibrin Mohammed, bayan sun kaikaici lokacin da aka watse daga fada, wadda ke da tazarar kilomita goma da marabar Gurku da ke jikin babbar hanyar da ta tashi daga Abuja ta dangana da Keffi, inda suka tafi da shi da mai ɗakinsa.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ta Nasarawa, Rahman Nansel, ya ce an yi wa rundunar `yan sanda ƙiran neman ɗauki a ranar 6 ga watan Agusta, cewa wasu da ake zargin masu satar mutane ne sun kai samame fadar mai martaba sarkin Gurku.
KU KUMA KARANTA: Ƴan bindiga sun kashe basarake sun ƙona gawarsa a Imo
Nan da nan kwamishinan `yan sanda ya tura jami’ansa zuwa fadar tare da haɗin-gwiwa da ƴan banga.
Suna isa suka tarar an sace sarkin da iyalinsa, kuma ba a san inda aka tafi da su ba. An karaɗe dazukan da ke kewaye amma ba a yi nasarar samun su ba.“
Kakakin ƴan sandan ya ce jami`ansu sun bazama, suna ƙoƙarin gano maɓoyar ‘yan bindigan don ceto basaraken da mai ɗakin nasa.
Jihar Nasarawa na maƙwabtaka da jihohi da dama da ke fama da ƙalubalen da ya shafi tsaro, ciki har da Binuwai da Filato da Kaduna da Kogi da kuma Abuja, babban birnin tarayya.
Ko a watan jiya, gwamnan jihar Abdullahi Sule ya nuna damuwa game da yadda miyagun da aka fatattaka a jihohi maƙwabta ke kwarara jiharsa. Har ma ya buƙaci hedikwatar tsaron Najeriya da ta taimaka wajen daƙile miyagun.
[…] KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun sace Sarki da iyalansa a jihar Nasarawa […]