No menu items!

Sample Page Title

Date:

Wasu ’yan bindiga a ranar Juma’a sun sace mutum 150, galibinsu mata da ƙananan yara a ƙaramar hukumar Maru ta jihar Zamfara.

Maharan sun kuma kashe mutum ɗaya a yankin yayin wani farmaki da ya ɗauki tsawon sa’o’i ana yi.

Harin dai na zuwa ne ƙasa da mako ɗaya bayan ’yan bindigar sun sace mutum 17 a ƙauyen Ruwan Ɗorawa na ƙaramar hukumar ta Maru.

Aminiya ta gano cewa maharan dai sun kai farmakin ne a ƙauyukan Mutunji da Kwanar-Dutse da Sabon-Garin Mahuta da kuma Unguwar Kawo.

Wani mazaunin ƙauyen Mutunji, wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce maharan sun kai farmakin ne wajen ƙarfe 9:00 na daren Juma’a, kuma sun ƙaddamar da hare-haren ne a ƙauyukan huɗu a lokacin ɗaya.

KU KUMA KARANTA: Jami’an tsaro sun kashe ’yan bindiga, sun ceto mutane a Katsina da Kaduna

Ya ce, “Suna shiga ƙauyen Mutunji suka fara harbi a sama domin su firgita jama’a. Nan take kuma mutanen suka fara gudun tsira da rayukansu.

“Daga nan ne sai suka shiga kama mutane masu rauni, galibinsu mata da ƙananan yara, saboda duk ƙarfafan garin su tsere.

“Lokacin da suke tsaka da kai harin ne na ƙira wani abokina a ƙauyen Kwanar Dutse da ke kusa da mu don neman taimako, inda ya shaida min su ma a lokacin harin ake kai musu. Ya ce min lokacin ma yana cikin daji bayan ya tsere da abokansa.

Shi ma wani mazaunin yankin da ya buƙaci a sakaya sunan nasa ya ce akwai yiwuwar maharan duka tare suke amma suka raba kansu gida huɗu, kowanne suna kai hari ƙauye ɗaya.

“Mun gano maharan sun ƙaddamar da hare-haren ne a ƙauyukan huɗu a lokaci ɗaya, inda daga bisani suka sake haɗuwa suka yi cikin daji da mutanen da suka kwasa.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...