‘Yan bindiga sun sace mata biyar da suka tafi biki a Katsina

0
168

A ƙalla mutane huɗu ciki har da ɗan sanda guda ɗaya ne aka kashe yayin da aka yi awon gaba da wasu da dama a lokacin da ‘yan ta’adda suka kai hari a Domawa a ƙaramar hukumar Ɗanmusa ta Jihar Katsina a daren ranar Alhamis. 

An kuma sace wasu ‘yan mata biyar da wani mutum ɗaya a wani hari na daban da aka kai Sukola, da ke ƙaramar hukumar Bakori a jihar. 

Jaridar Premium Times ta ambato wata majiya na cewa ‘yan ta’addan sun kai hari a cikin ƙauyen na Domawa ne ‘yan mintuna kaɗan bayan ƙarfe 9:00 na dare. 

“Yan ta’addan sun shiga cikin ƙauyen inda suka fara harbi ba ƙaƙƙautawa domin tsoratar da mutane. 

KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga na bautar da mutane a jihar Katsina

Mutum ukun da ‘yan ta’addan suka kashe, ‘yan ta’addan sun ɗauke su a matsayin barazana, domin a lokacin da (‘yan ta’addan) suka ce su bi su, sai suka ƙi.” 

Ya bayyana sunayen waɗanda aka kashe a matsayin Sa’idu Mai Kyaran, Na Doguwa da Suyudi Mai Tabarma yayin ya ce sunan ɗan sandan Hassan.

A yankin kudancin jihar Katsina, ‘yan ta’addan sun kai wani hari da ya kai ga yin garkuwa da wasu ‘yan mata biyar da suke halartar wani bikin ɗaurin aure a ƙauyen Sukola.

Wani shugaban matasa a ƙauyen da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa “Su (‘yan matan) sun fito ne daga ƙauyuka daban-daban da ke kewayen Sukola. 

Sun je ƙauye ne domin taya murna ga wata ƙawarsu da za a yi bikinta a ranar Asabar. 

Kun san mata suna da shagulgulan da suke kafin ɗaurin aure, bayan an tashi shagalin dare ne ‘yan ta’adda suka far wa ƙauyen.” 

Ya bayyana sunayen ‘yan matan da aka sace matsayin Maryam Sani, Maijidda Kabir, Abida Matthew da Maryam Ibrahim. 

Ya ce bai san sunan ta ƙarshen su ba. A yayin harin da aka kai da misalin ƙarfe 11:00 na dare, majiyar ya ce ‘yan ta’addan sun zo ne da “makamai da dama,” inda suka toshe duk wata hanyar shiga cikin ƙauyen tare da ci gaba da harbe-harbe domin haifar da ruɗani. 

Legit Hausa ta tuntubi muƙaddashin kakakin rundunar ‘yan sanda jihar Katsina, Abubakar Sadiq, domin samun ƙarin bayani kan ƙoƙarin da ake wajen ceto ‘yan matan, bai dawo da saƙon da aka tura masa ba har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.

Leave a Reply