‘Yan bindiga sun sace mahaifin ɗan majalisa a Zamfara

1
313

Wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki ƙauyen Kasuwar Daji dake ƙaramar hukumar Ƙaura Namoda a jihar Zamfara inda suka yi awon gaba da Uban ƙasar garin Alhaji Ibrahim S/Fada Kasuwar Daji, Uba ga Ɗan Majalisar Dokokin Jihar Zamfara mai ci Hon. Anas S. Fada Ƙaura. 

Rahotanni daga ƙauyen sun bayyana cewa, lamarin ya faru ne da sanyin safiyar jiya Alhamis da misalin ƙarfe 2:30 zuwa 3:00 na dare inda ‘yan bindigar suka yi harbi biyu a saman iska kafin su tafi da shi. 

Zuwa haɗa wannan rahoton dai babu wani labari game da shi kuma ba a san halin da yake ciki ba.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun harbe ɗan sanda a Ibadan

1 COMMENT

Leave a Reply