No menu items!

Sample Page Title

Date:

Wasu ‘yan bindiga da har yanzu ba a tantance su waye ba, sun yi garkuwa da ɗaliban jami’ar Jos su bakwai.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Alfred Alabo, ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) aukuwar lamarin a ranar Laraba a garin Jos.

A cewar Alabo, an sace ɗaliban ne a ranar Litinin da daddare a masauƙinsu da ke wajen harabar jami’ar.

Ya bayyana cewa an sace ɗaliban ne a lokacin da suke karatun jarabawar zango na biyu, wanda aka fara a ranar Talata.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun kashe Fasto da mutane 20 a Filato

“Gaskiya ne wasu miyagu sun yi awon gaba da ɗalibai bakwai na jami’ar Jos.

“An sace su ranar Litinin da misalin ƙarfe 8:30 na dare a hostel ɗin su, dake kan titin Bauchi ring road a ƙaramar hukumar Jos ta Arewa.

“Kwamishanan ‘yan sandan jihar Bartholomew Onyeka, ya tura jami’an ‘yan sanda ɗauke da makamai domin kamo masu garkuwa da mutane tare da tabbatar da ganin an sako ɗaliban da aka sace.

“Operation Safe Haven (OPSH), da hukumomin tsaro sun kuma tura jami’ansu domin gudanar da bincike da ceto,” inji shi.

Mista Alabo ya shawarci ɗalibai da mazauna yankin da su kwantar da hankalinsu, yana mai jaddada cewa jami’an tsaro suna bakin ƙoƙarinsu wajen ganin an dawo da ɗaliban da aka sace cikin gaggawa.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

2 COMMENTS

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...