Wasu ‘yan mahara da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun kashe ‘yan uwa biyu a ƙauyen Gajere da ke ƙaramar hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna.
Lamarin dai a cewar majiyoyin ya faru ne da safiyar Juma’a a yayin da waɗanda abin ya shafa ke aiki a gonakinsu.
Sagir Umar, wani mazaunin yankin, wanda ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin, ya nuna matuƙar damuwarsa kan yadda ‘yan fashin ke ƙaruwa.
KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da babban Limami a jihar Ondo
Umar ya bayyana cewa aƙalla mutanen ƙauyen 10 ne ‘yan bindigar suka yi garkuwa da su a cikin makonni biyu da suka gabata.
Ya ce ‘yan bindigar sun daɗe suna tafka ɓarna a cikin al’umma ta hanyar yin garkuwa da mutanen da ba su ji ba ba su gani ba tare da sace musu dabbobi.
Haka kuma ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Kakangi a majalisar dokokin jihar Yahaya Musa ya tabbatar da kisan na baya bayan nan.
Yayin da yake jajanta wa waɗanda abin ya shafa da iyalansu, ɗan majalisar ya nuna baƙin cikinsa kan lamarin.
Ya kuma bayyana cewa ‘yan bindigar sun sace wasu manoma biyu a ƙauyen Gwanda Mai Gyaɗa a ranar Alhamis yayin da suke aikin gonakinsu.
Sai dai ya yaba da yadda ake gudanar da aikin tsaro a hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari. Ya bayyana ƙauyukan Kutemeshi, Tabanni, Kuyello, da Dogon Dawa a matsayin wuraren da aka ga ‘yan fashin.
Da aka tuntuɓi jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Mohammed Jalige, ya yi alƙawarin zai sake ƙiransa bayan samun ƙarin bayani kan lamarin.
Har yanzu dai bai cika alƙawarin ba har zuwa lokacin da ake gabatar da wannan rahoto.
[…] KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun kashe ‘yan uwa biyu a Kaduna […]