Rundunar ‘yan sanda a jihar Bauch ta tabbatar da cewa wasu ‘yan bindiga sun kashe mutum ɗaya tare da yin garkuwa da wasu mutane uku ciki har da shugabannin al’umma biyu a ƙaramar hukumar Ningi da ke jihar.
Kakakin rundunar, SP Ahmed Wakil, ya tabbatar da hakan a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya a ranar litinin a birnin Bauchi.
Ya ce ‘yan bindigar sun kai hari a wata al’umma da aka fi sani da Balma, inda suka kashe mutum ɗaya tare da yin garkuwa da wasu mutane uku, ciki har da shugabannin al’umma biyu da yammacin ranar asabar.
KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun sace yarinya ‘yar shekara 7 a Abuja
Wakil ya ce shugabannin al’ummar biyu, wani hakimin ƙauye ne a yankin Balma da kuma hakimin unguwar Bakutunbe da kuma wani mutum ɗaya da aka yi garkuwa da su.
Kakakin ya ce a ranar lahadin da ta gabata ne rundunar ta samu rahoto daga ofishinta na Balma cewa ‘yan bindiga sun kai hari ƙauyen.
“Sun yi harbin lokaci-lokaci sannan suka tafi da hakimin ƙauyen, Hussaini Saleh, mai shekaru 48.
Wakil ya ce an sace hakimin ƙauyen ne tare da wani Idris Mai Unguwa da wani mutum mai suna Ya’u Gandu Maliya, mai shekaru 45.
“Duk da haka ‘yan bindigar sun harbe wani Haruna Jibrin a kai. “Lokacin da ’yan sanda suka samu ƙiran gaggawa, an shirya wata tawaga zuwa wurin, inda suka ceto wanda abin ya shafa, suka garzaya da shi babban asibitin Ningi inda yake jinya amma daga baya aka tabbatar da mutuwarsa.
“A halin yanzu, ‘yan sanda a sashin Ningi suna sintiri daji, suna ƙoƙarin ganin yadda za su kuɓutar da shugabannin al’ummar biyu da aka sace da ransu.”
Kakakin ya yi ƙira ga ‘yan ƙasar da su riƙa bayar da bayanai kan yadda mutane ke tuhume-tuhume ga hukumomin tsaro domin ɗaukar matakin gaggawa.
[…] KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun kashe mutum ɗaya, sun sace Hakimai biyu a Bauchi […]
[…] KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun kashe mutum ɗaya, sun sace Hakimai biyu a Bauchi […]