Wasu ‘yan bindiga daga ƙungiyoyin miyagu sun kashe mutane 25 a lokacin da suka kai farmaki a wasu ƙauyuka huɗu a yankin arewa maso yammacin Najeriya, a matsayin ramuwar gayya saboda farmakin da sojoji suka kai maɓoyarsu, a cewar wani jami’in tsaro a yankin.
A Katsina aka kai hare-haren a ranar Alhamis, jihar da ke daga cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya da ke fama da hare-haren ‘yan bindiga masu yin garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa.
‘Yan bindiga sun auka ƙauyukan Unguwar Sarki, Gangara, Tafi da Kore a ƙaramar hukumar Sabuwa da yammacin ranar Alhamis, inda suka buɗe wuta kan mazauna ƙauyukan, a cewar Nasiru Babangida, kwamishinan tsaro na jihar Katsina.
KU KUMA KARANTA:Harin ‘yan bindiga ya sabbaba kisan mutane 10 da yin garkuwa da masu unguwanni 2 a Kaduna
Mazauna yankin da dama sun jikkata yayin da ‘yan bindigar suka yi garkuwa da su, a cewar Babangida.
Yawancin garuruwa a yankin arewa maso yammacin Najeriya sun kafa rundunonin mayaƙan sa-kai ko ‘yan banga domin yaƙar ‘yan bindiga a yankunan karkara da babu jami’an tsaro sosai, kuma ɓangarorin biyu na fafatawa sosai.
A baya-baya nan ‘yan bindigar sun kai farmaki a ƙauyukan ne a matsayin ramuwar gayya saboda hare-hare ta sama da sojojin Najeriya suka kai sansanoninsu a yankin da kuma a maƙwabciyar jihar Kaduna, lamarin da ya yi sanadin mutuwar sama da ‘yan bindigar 200, inji Babangida.
Ƙungiyoyin da suka ɓoye a dazuzzukan jihohin Zamfara, Katsina, Kaduna da Neja, sun yi ƙaurin suna wajen sace ɗalibai da yawa a makarantu a shekarun baya-baya nan.