‘Yan bindiga sun kashe basaraken gargajiya da ‘ya’yansa huɗu, sun sace shanu 100 a Kaduna

Wasu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun kashe wani mai riƙe da sarautar gargajiya, mai suna Arɗo na Birni da Kewaye na Masarautar Zazzau, Shuaibu Mohammed tare da ‘ya’yansa huɗu. Lamarin ya faru ne a daren ranar asabar da misalin ƙarfe 10 na dare a ƙauyen Ɗorayi da ke ƙaramar hukumar Zariya a jihar Kaduna.

‘Yan fashin sun kuma yi awon gaba da shanu 100 na mamacin.

Matar marigayin, Malama Halima Shuaibu ta shaida wa manema labarai bayan jana’izar waɗanda aka kashen cewa ‘yan bindigar sun harbe mijinta a kai.

“An fito da Arɗo daga ɗakin kwanansa, aka harbe shi har sau biyu, kuma ya mutu nan take.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun kashe ‘yan uwa biyu a Kaduna

“’Yan bindigar sun bi ɗaki-ɗaki a cikin harabar gidan inda suka kashe ‘ya’yana huɗu da suke da aure da ‘ya’ya.

“Waɗanda aka kashe su ne Adamu Shuaibu, Musa Shuaibu, Abubakar Shuaibu da Ibrahim Haruna.

“Bayan sun kai hari harabar gidan, sun kuma tafi da shanu sama da 100,” in ji ta.

Mutum ɗaya tilo da ya tsira daga harin a cikin yaran Arɗo, Abdurrahman Shuaibu ya ce ‘yan bindigar sun harbe wasu mutane biyu a hanyarsu ta fita daga ƙauyen.

Da aka tuntuɓi Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, DSP Mohammed Jalige, ya ce har yanzu ba a yi masa bayani kan lamarin ba.


Comments

3 responses to “‘Yan bindiga sun kashe basaraken gargajiya da ‘ya’yansa huɗu, sun sace shanu 100 a Kaduna”

  1. […] KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun kashe basaraken gargajiya da ‘ya’yansa huɗu, sun sace shanu 100 a Kaduna […]

  2. […] KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun kashe basaraken gargajiya da ‘ya’yansa huɗu, sun sace shanu 100 a Kaduna […]

  3. […] KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun kashe basaraken gargajiya da ‘ya’yansa huɗu, sun sace shanu 100 a Kaduna […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *