No menu items!

Sample Page Title

Date:

’Yan bindiga sun sace gomman mahalarta biki a wani hari da suka kai ƙauyen Gidan Kunkun da ke gundumar Dawaki a ƙaramar hukumar Ƙauru ta Jihar Kaduna.

Wani jami’in tsaron sa-kai ya shaida wa Aminiya cewa an kashe mutum ɗaya lokacin harin da aka kai ana tsaka da shagalin bikin aure.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, matashin da aka kashe mai shekaru 24 ɗan uwan amaryar da ake bikin auren nata ne.

Tuni dai an kai gawarsa ƙaramar hukumar Ikara domin yi masa jana’iza, yayin da mutane ukun da suka jikkata — Iliyasu Ibrahim da Zaphaniya Danbala da Victor Audu — suke samun kulawa a babban asibitin garin Kauru.

Daga cikin waɗanda aka tabbatar cewa ’yan bindigar sun yi awon gaba da su akwai Josia Sama’ila da Adamu Bulus da Enoch Bulus da Enoch Ibrahim da Yahuza Sama’ila da Lawan Francis da wani fasto a cocin Heken da ke ƙauyen na Gidan Kunkun da kuma wasu matan aure kimanin 10 da ’ya’yansu.

KU KUMA KARANTA: Yadda ’yan bindiga suka kashe mutum 4 suka sace 39

Bayanai sun ce ya zuwa yanzu dai fargaba ta lafa yayin da mutanen garin sun koma ci gaba da harkokinsu.

Aminiya ta tuntuɓi kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, ASP Mansir Hassan wanda ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya bayyana cewa sun ɗauki matakin ganin cewa sun ƙwato mutanen da aka ɗauke nan ba da daɗewa ba.

Kazalika, ASP Mansir ya yi ƙira ga al’umma da su riƙa sa ido a kan masu kai-komo a yankinsu.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...