Rundunar ‘yan sanda a jihar Kaduna a ranar asabar ɗin da ta gabata ta tabbatar da kashe mutane bakwai a lokacin da suke gudanar da sallah a wani masallaci da ke ƙauyen Saya-Saya da ke ƙaramar hukumar Ikara.
Mai magana da yawun rundunar, Mansir Hassan, ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya aukuwar lamarin.
Mista Hassan, mataimakin sufeton ‘yan sanda, ya ce “da misalin ƙarfe 8:00 na dare a ranar Juma’a, mun samu labari daga ƙauyen Saya-Saya cewa an kashe mutane shida a lokacin da suke yin sallar Isha’i a wani Masallaci. “
’Yan bindigar kimanin tara ne a kan babura, sun isa wurin suka far wa mutanen da ke cikin Masallacin.
KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun kai hari a Abuja, sun yi awon gaba da wani magidanci
“A wajen, sun harbe mutane shida yayin da suke addu’a a wani masallaci a ƙauyen.”
Malam Hassan ya ce ‘yan bindigar sun kuma koma wani masallaci da ke Tashar Dauda, shi ma a ƙaramar hukumar Ikara, inda suka kashe mutum ɗaya yayin da uku suka samu raunuka.
Ya ce ɓarayin sun tafi da babura huɗu. “Da samun labarin, sai jami’in ‘yan sanda reshen Ikara ya garzaya da jami’an tsaro zuwa wurin da lamarin ya faru.
“A lokacin da mutanenmu suka isa wurin, ‘yan bindigar sun tsere cikin daji kafin isowar jami’an tsaro.
Ya zuwa yanzu, ba a kama wani mutum a wurin da lamarin ya faru ba, amma an ƙwato harsashi biyar na bindiga ƙirar AK49.
Ya ce an miƙa gawarwakin bakwai ga ‘yan uwansu. Daga cikin mutane ukun da suka jikkata, ya ce an kai biyun zuwa babban asibitin Tudun-Wada da ke jihar Kano, yayin da ɗaya ke kwance a babban asibitin Ikara.
Hassan ya ce ‘yan sanda sun ƙara zage damtse wajen cafke waɗanda ake zargin tare da hukunta su.
Ya ƙara da cewa kwamishinan ‘yan sanda, Musa Garba, yana ƙira ga ‘yan ƙasar da su riƙa kai rahoton duk wani abu da ba a saba gani ba da kuma shakku ga hukumomin tsaro mafi kusa domin ɗaukar matakin da ya dace.
[…] KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun kai hari a masallacin Kaduna, sun kashe mutane bakwai […]