‘Yan bindiga sun harbe ɗan sanda a lokacin da yake saduwa da budurwar sa a daji

Wani ɗan sanda mai suna Judas Chiloane, ya rasa ransa a lokacin da ya je tsaka da yin jima’i da masoyiyarsa a wani daji a yankin Mpumalanga na ƙasar Afirka ta Kudu.

A cewar kafar sadarwa ta Harare a ranar Alhamis, wasu ‘yan bindiga daɗi sun harbe ɗan sandan har sau biyu a kujerar baya ta motarsa ƙirar Ford Ranger bakkie yayin da masoyiyar sa bats samu rauni ƙo kaɗan daga harbin ba.

Rundunar ‘yan sandan Afrika ta Kudu ta kama Charles Mbungeni Mabuza da Howard Mashego a ranar Litinin da ta gabata kan laifin kisan ɗan sandan.

KU KUMA KARANTA: Likitan da yayi wa ƙanwar matarsa ‘yar shekara 15 fyaɗe ya ce ba budurwa ba ce inji shaidu

Kakakin rundunar ‘yan sanda na musamman, Captain Dineo Sekgotodi, ya ce mutanen biyun sun ce sun je wurin ne domin yiwa masoyan fashi, da ke yawan zuwa wurin domin yin lalata a cikin mota, yana mai cewa, “Mutane biyun sun shaida mana cewa za su je wurin da ke kusa da titin Graskop, inda aka harbe Chiloane don yiwa masoyan fashi, waɗanda da ke amfani da yankin don yin jima’i a cikin motarsu.

A cewar Sekgotodi, ‘yan fashin guda biyu da ake zargin sun yi wa Chiloane kwanton ɓauna ne inda suka ƙwace bindigarsa, suka kuma harbe shi a cinyarsa. Lokacin da matar ta bukaci a taimaka, ‘yan sanda sun isa inda aka kashe abokin aikinsu, don kai masa ɗuaki.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *