‘Yan bindiga sun ƙara sace ɗaliban jami’ar Zamfara

’Yan bindiga ɗauke da makamai a yammacin ranar Asabar sun sake yin garkuwa da wasu ɗaliban Jami’ar Tarayya Gusau da ke Jihar Zamfara.

Ɗaliban biyu, a cewar wani shaidan gani da ido, maza da mata ne, waɗanda aka yi garkuwa da su a ɗakin kwanan ɗaliban da ke kusa da jami’ar da misalin ƙarfe 9 na daren ranar Asabar a unguwar Sabon Garin Damba da ke Gusau, babban birnin jihar.

Mazauna yankin sun ce ‘yan bindigar sun mamaye al’ummar ne ‘yan mintoci kaɗan bayan ƙarfe 8 na dare inda suka yi ta harbin kan mai uwa da wabi don tsorata mazauna yankin.

Jami’an tsaro sun yi ta harbin bindiga da dama inda suka yi ƙoƙarin fatattakar ‘yan ta’addar amma ‘yan fashin sun tafi da ɗalibai biyu.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun kai hari kan ‘yan kasuwa a Taraba

Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa saboda dalilai na tsaro ya shaida wa ‘News Point Nigeria’ cewa haɗin gwiwar jami’an tsaro na ‘yan sanda da sojoji na nan a hannun ‘yan fashin.

Ƙoƙarin yin magana da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Yazid Abubakar, bai yi nasara ba domin bai amsa ƙiran da aka yi masa ba.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *