No menu items!

Sample Page Title

Date:

Rahotanni sun bayyana cewa wasu ‘yan bindiga sanye da hijabi sun kai hari a ofishin ‘yan sanda da ke ƙauyen Saki Jiki da ke ƙaramar hukumar Batsari a jihar Katsina, inda suka kashe jami’in ɗansanda guda.

Kakakin Rundunar ’yan sandan jihar, Abubakar Aliyu, wanda ya tabbatar wa manema labarai hakan a ranar Juma’a, 19 ga watan Janairu, 2024, ya ce wani ɗansanda ya samu rauni a harin.

Ya ce lamarin ya faru ne da ƙarfe 8 na daren ranar Alhamis, 18 ga watan Janairu.

KU KUMA KARANTA: ’Yan bindiga sun tarwatsa ƙauyuka 10 a Kaduna

“Jiya (Alhamis) da misalin ƙarfe 8:00 na dare wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sanye da hijabi, sun kai wa jami’an hari a ofishinsu dake ƙauyen Saki Jiki na ƙaramar hukumar Batsari,” in ji PPRO.

“Jami’an sun mayar da martani cikin jarumtaka tare da samun nasarar daƙile harin, amma jami’i ɗaya ya rasa ransa, wani kuma ya samu rauni sakamakon harin.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...