‘Yan bindiga na cigaba da ɗaukar rayuka a jihar Neja

0
196

Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Neja na bayyana cewa wasu ƴan bindiga sun halaka mutum 21 ciki har da magajin gari a ƙauyen Madaka da ke ƙaramar hukumar Rafi a jihar Neja.

Mazauna yankin sun shaida wa jaridar Premium Times cewa ƴan bindigan sun yi awon gaba da adadi mai yawa na mutane, waɗanda har yanzu ba a tantance yawansu ba.

A cewar majiyoyin, ‘yan bindigar sun kuma kona gidaje da shaguna kusan 50, da kuma motoci da babura da dama yayin wannan mummunan harin.

Yadda ƴan bindiga suka yi ɓarna Sun ce ‘yan bindigar dauke da muggan makamai sun shiga kauyen kana suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi, kafin daga bisani su fara kashe-kashe da ƙone-ƙone.

KU KUMA KARANTA: An kuɓutar da almajirai 18 da ‘yan bindiga suka sace a Sakkwato

Wani mazaunin ƙauyen ya ce saboda babu jami’an tsaro kauyen shiyasa ƴan bindigan suke shiga su yi abin da ransu ya so babu mai ɗaga masu yatsa.

Hakimin yankin, Isah Bawale, ya tabbatar da faruwar lamarin ga wakilin jaridar a Minna, babban birnin jihar, a wata tattaunawa ta wayar tarho.

An tattaro cewa shekara ɗaya da ya gabata, ƴan bindiga sun kai farmaki wannan kauyen kuma sun kashe magajin garin.

Da aka tuntubi jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Wasiu Abiodun, ya ce yana ci gaba da kokarin tantance rahotannin abin da ya faru a harin.

Kwamishinan tsaro na jihar, Bello Mohammed, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma ce gwamnati na kokarin tsare dukkan garuruwan da ke noma a jihar.

Leave a Reply