’Yan bindiga a Zamfara sun sace Hakimi da Limami

0
138

’Yan bindiga sun yi awon gaba da hakimin Rakyabu, Magaji Sa’idu da kuma babban limamin ƙauyen, Malam Abdullahi, da ke ƙaramar Hukumar Tsafe a Jihar Zamfara.

Lamarin ya faru ne a ranar Larabar da ta gabata lokacin da ’yan ta’addan suka kai hari ƙauyen, amma har yanzu ‘yan sandan ba su tabbatar ba.

Kakakin ’yan sandan Zamfara, Yazid Abubakar, ya shaida wa Aminiya cewa, “Ba ni da labarin faruwar lamarin, na dawo daga tafiya ne, amma zan tuntuɓi DPO na Tsafe.”

Amma wani mazaunin yankin ya ce maharan sun buƙaci al’ummar ƙauyen su ba su naira miliyan biyar a matsayin kuɗin fansa.

A cewarsa, al’ummar ƙauyen dubu 500 suka iya haɗawa domin biyan fansar hakimin da limamin, wanda maharan suka karɓa amma suka ƙi sako shi.

“Sun ce dole ne mu cika ragowar naira miliyan 4.5, ba su saki waɗanda suka sace ba har yanzu.

“Muna neman tallafi daga hukumomin da abin ya shafa don taimaka mana wajen ganin waɗanda aka sace sun kuɓuta, mun yi iya ƙoƙarinmu tun makon da ya gabata.”

KU KU KUMA KARANTA: Remi Tinubu ta miƙa ɗaliban da aka sace a Jami’ar Dutsin-Ma hannun iyayensu

‘Yan bindiga sun daɗe suna ta’addanci a wasu jihohin Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya, inda suke kai hare-hare tare da sace mutane domin neman kuɗin fansa.

A yankin Arewa Maso Gabas kuwa an fatattaki mayakan Boko Haram da suka jima suna kashe mutane.

Fiye da mutane 40,000 ne aka kashe tare da raba miliyan biyu da muhallansu tun daga 2009 zuwa yanzu.

Leave a Reply