‘Yan bindiga a Kaduna sun kashe wani likita da sace mutane 8

0
70
'Yan bindiga a Kaduna sun kashe wani likita da sace mutane 8

‘Yan bindiga a Kaduna sun kashe wani likita da sace mutane 8

Daga Ali Sanni Larabawa

‘Yan bindiga sun kashe wani likita tare da sace wasu mutane 8 a garin Kwassam da ke ƙaramar hukumar Kauru a jihar Kaduna.

‘Yan bindigar sun kashe wani likita tare da yin garkuwa da wasu mutane 8 a garin Kwassam da ke ƙaramar hukumar Kauru a jihar Kaduna.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, ɗan majalisar tarayya na Mazabar Kauru, Hon. Zakari Ahmad Chawai, ya ce ana yawan samun hare-haren akai akai a mazaɓun Kwassam da Dawaki dake ƙaramar hukumar ta Kauru.

“Kwanaki huɗu da suka wuce ’yan bindigar sun kai hari a wata unguwa dake cikin mazaɓar Dawaki inda suka sace wasu mazauna yankin, kuma jiya sun sake kai hari a unguwar Kwassam,” in ji shi.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga a Binuwai sun ƙona gidaje 23

Yace, masu garkuwa da mutanen sun kashe mutun ɗaya, sun sace mutane 8 kuma sun tafi da wasu kayayyakin mutane da ba’a tantance adadinsu ba.

Hon. Chawai ya yi ƙira ga jami’an tsaro da su ƙara ƙaimi wajen magance hare-haren dake yawan faruwa a yankunan Kwassam da Dawaki.

Rahotanni sun nuna cewa mazauna yankin suna ci gaba da gudanar da ayyukansu na yau da kullum kamar yadda suka saba bayan lafawar abin.

Sai dai har yanzu babu wani bayani daga masu garkuwar kan batun kuɗin fansa, kamar yadda wani mazaunin Kwassam ya shaidawa manema labarai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here