Sarkin Kano na 14 Muhammadu Sanusi II, a ranar Laraba, ya kai wata ziyara mai cike da tarihi a tsohon birnin Kano, tun bayan shekaru uku da sauke shi daga muƙaminsa na sarkin Kano.
An tsige Sanusi, Sarkin Kano na 14 a ranar 9 ga Maris, 2020, bisa zargin rashin biyayya, daga bisani Gwamnan Jihar Kano, Umar Ganduje ya kore shi zuwa Awe, a jihar Nasarrawa.
Sarkin, a ziyararsa, Ya isa filin jirgin sama na Malam Aminu Kano ranar Laraba, ya kuma wuce kai tsaye gidan mahaifiyarsa, dake kan titin Ibrahim Dabo a birnin Kano kamar yadda wani faifan bidiyo ya nuna cewa tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), a cikin cikakken kayan sarauta, an gansa yana musabaha tare da tawaga daban-daban na ‘yan uwa da masu riƙe da muƙaman gargajiya da kuma masu hannu da shuni da sauran masu yi masa biyayya da nuna masa ƙauna da soyayya.
KU KALLI BIDIYON ANAN:
Wata majiyar da ba ta so a bayyana sunanta, ta bada tsegumin cewa tsohon sarkin na kan hanyarsa ne na kai ziyara zuwa Dutse, babban birnin jihar Jigawa, domin kai ta’aziyya a majalisar masarautar Dutse, bisa rasuwar Sarkin Dutse, mai shekaru 78 a duniya, wato Marigayi Muhammad Nuhu Sanusi.
A cikin ziyarar tasa a garin Dutse, Sanusi, wanda jagora ne a ɗarikar Tijjaniyya a Najeriya, ya kai ziyarar ban girma ga sabon Sarkin Dutse, Hameem Nuhu Sanusi.