Yadda yaro ɗan shekara 20 ya sace mahaifiyarsa, ya karɓi kuɗin fansa naira miliyan 30 a Zamfara

3
507

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta kama wani yaro ɗan shekara 20 bisa zarginsa da shirya sace mahaifiyarsa da wasu mutane uku tare da karɓar kuɗin fansa naira miliyan talatin.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Mohammed Shehu, a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Gusau, babban birnin jihar a ranar Juma’a, ya ce wanda ake zargin, Thomas Yau, ya sanar da ‘yan sanda cewa ya haɗa baki da wasu mutane huɗu, kuma kowanne daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da su ya biya naira miliyan 10 , ciki har da mahaifiyarsa.

Shehu ya ce, “A ranar 12 ga Fabrairun 2023, rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, ta hanyar aikin ‘yan sanda na al’umma, ta ɗauki matakin gano bayanan sirri da suka kai ga fashewar wata ƙungiyar masu garkuwa da mutane, tare da cafke wasu mutane shida da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, waɗanda suka addabi ƙauyuka daban-daban a Kaduna, Kano da sauran jihohin da ke makwabtaka da su, kamar Zamfara da Sakkwato.

KU KUMA KARANTA:Yadda ɗa ya sace mahaifinsa, ya karɓi kuɗin fansa naira miliyan biyu da rabi

“A binciken da ake yi, an gano cewa waɗanda ake zargin sun yi garkuwa da mutane da dama, inda aka yi garkuwa da mutane da ba a tantance adadinsu ba, aka kuma karɓi miliyoyin naira a matsayin kuɗin fansarsu.

“Kowane wanda ake tuhuma ya
ƙara ba da labarin yawan sace-sacen da ya yi, da kuma irin rawar da ya taka a kowane aiki.

“Abin mamaki, ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin, Thomas Ya’u, ya furta cewa, a shekarar da ta gabata, shi ne ya kitsa sace mahaifiyarsa da wasu mutane guda uku.

“Sun karɓi naira miliyan 30 daga hannun ‘yan uwansu a matsayin kuɗin fansa, sannan aka ba shi miliyan ɗaya a matsayin kasonsa.”

Shehu ya ci gaba da cewa, ana kan bincike kan lamarin kuma za a gurfanar da waɗanda ake zargin.

3 COMMENTS

Leave a Reply