Yadda ‘yan bindiga suka sace mutane 9 a rukunin gidajen alfarma a Abuja

0
262

Aƙalla mutane 9 ne ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a rukunin gidajen alfarma na Grow Homes da ke Kuchibiyi a yankin Kubwa a babban birnin tarayya Abuja.

‘Yan bindigar sun kai kimanin 20, an ce sun kai farmaki ne da misalin karfe 11:30 na daren Juma’a.

Wani mazaunin unguwar da ya bayyana sunansa da Hassan ya ce ‘yan bindigar sun yi garkuwa da waɗanda abin ya shafa ne daga wasu gidaje guda biyu a unguwar.

Ya ƙara da cewa lamarin ya haifar da firgici a cikin al’umma. “A jiya, (Jumma’a), da misalin karfe 11:30 na dare wasu ‘yan bindiga da yawa sun zo domin gudanar da wani samame a rukunin gidajen alfarma na Grow Homes dake Kuchibiyi.

“Mun ji ƙarar harbe-harbe kuma an ɗaukacin jama’ar da ke nan sun firgita.

“Da safiyar yau, mun je gidan ne muka samu labarin cewa ‘yan bindigar sun kai kimanin 20, sun yi da kewayawa daga wani gida zuwa wancan, suna kora mazauna gadijen.

KU KUMA KARANTA: Yadda ‘yan bindiga sun kai farmaki makarantar firamare, suka yi awon gaba da ɗalibai

Haka kuma sun yi garkuwa da aƙalla mutum 9, ciki har da yara da mata daga wasu gidaje biyu a yankin.

“Sun tsere ne ta cikin daji da ke da alaƙa da ƙauyen Paze” in ji shi.

Tun da safe jami’an ‘yan sanda da jami’an tsaro sun fara bincike a daji domin ganin ko za su iya kuɓutar da mutanen da aka yi garkuwa da su.

Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sanda a Abuja, SP Josephine Adeh, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce ‘yan sanda da jami’an tsaron gidaje suna kai komo a dazuzzukan yankin domin ceto wadanda lamarin ya shafa.

Adeh ta ce, “Bayan samun kiran gaggawar, nan take muka tura mutanenmu wurin, sai dai waɗanda ake zargin sun tafi da wasu da abin ya shafa zuwa cikin daji.

“Rundunar ‘yan sanda da jami’an tsaro na ci gaba da sintiri a daji a yankin domin ganin an ceto su.”

Ta kuma buƙaci mazauna yankin da kada su firgita, su taimaka wa ‘yan sanda da sahihan bayanai da za su kai ga cafke maharan.

Adeh ta ƙara da cewa “Muna ƙira ga mazauna garin da su kwantar da hankalinsu tare da bayar da bayanai masu amfani da za su kai ga kama waɗannan masu laifin.”

Leave a Reply