Yadda ta kasance a babbar kotun Kano kan sauraren ƙarar da Mal. Abduljabbar ya shigar

0
425

Babbar kotun jiha da ke nan Kano ta sanya ranar 12 ga Fabrairu domin sauraron ƙarar da Sheikh Abduljabbar ya shigar yana ƙalubalantar hukuncin kisa da aka yanke masa.

Wani ɗalibin Malamin Musa San Turaki Fali daga jihar Bauchi ne ya shigar da ƙarar a madadin malamin.

Sai dai bayan zaman da aka yi a jiya litinin lauyan gwamnati ya nemi da a bashi lokaci domin nazartar ƙarar, yayin da shima lauyan wanda ya shigar da ƙarar ya nemi ƙarin lokacin.

Hakan ce ta sanya mai shari’ar bayan nazartar dukkanin ɓangarorin biyu ya sanya ranar 12 ga Fabrairu domin saurarar batun.

Leave a Reply