Sunansa Aliyu Abdullahi Bala. Ya bar Jos, Jihar Filato, Najeriya a ranar 23 ga Fabrairu 2021, zuwa ƙasar Saudiyya, inda ya bi ta Nijar, chad da Sudan, ya kuma isa ƙasar Saudiyya ne a ranar 10 ga watan Disamba 2022.
A kan hanyar sa ya ci karo da ƙalubale da dama da suka da haɗa da shahararriyar ƙungiyar Boko Haram, masu garkuwa da mutane, ‘yan fashi da makami, dabbobi masu haɗari da dai sauransu.
Ko da yake ’yan Boko Haram ba su tsananta masa ba amma sun nemi ya yi musu addu’a. ‘Yan bindiga ne kawai suka ƙwace wayarsa tunda bashi da kuɗin da zai basu, sai dai da isowarwa sa wani ƙaramin gari a ƙasar Sudan, sai ya ba da labarin irin wahalar da ya sha, inda suka tausaya masa, suka ba shi kuɗi, suka sayo masa sabuwar waya.
KU KALLI BIDIYON SAUKARSA SAUDIYYA ANAN:https://bit.ly/3VXt9N8
A tafiyarsa zuwa Makka, ya sha ƙwana a cikin daji a lokuta da dama, wani lokaci yakan tura keken saboda tayoyin sun fashe.
A duk garuruwa da ƙauyuka da ya ratsa, an yi ta yaba masa a matsayin jarumi tare da bashi kuɗaɗe da kuma fatan alheri.
Yanzu haka yana Makkah inda yaje yake yin Umrah, kuma zai tafi Madina don ziyartar masallacin Annabi (SAW) inda zai zauna a can tsawon mako guda, daga nan kuma zai koma Jiddah, sannan zai ya koma gida Najeriya.
[…] KU KUMA KARANTA: Yadda mutumin da ya yi tattaki daga Najeriya zuwa Saudiyya a kan keke yayi karanbatta da ‘yan Boko… […]