Yadda bacci ta gefen hagu ke illata zuciyar mutum

A cewar wata ƙasida da aka wallafa a mujjalar Healthline, wacce ta yi duba kan illar da bacci a gefen hagu ke haifarwa ga lafiyar zuciya.

Masu bincike sun gano cewa barci a gefen hagu na mutum yana tayar da hawan jini a cikin zuciya, wanda zai iya haifar da mummunan sakamako na lafiya.

Yawancin masu bincike a shekarar 1997 sun gano cewa lokacin da aka yi amfani da electrocardiograms don saka idanu akan ayyukan zuciya, akwai bambance-bambance masu ban mamaki lokacin da mutum ya kwanta barci a gefen hagu da damansa.

KU KUMA KARANTA: Yadda aya ke ƙara karfin jima’i da kuma hana tsufa da kawar da ciwon siga

Idan kuna yawan yin barci a gefen hagunku, kuna iya la’akari da canzawa zuwa wani wuri na barci daban wanda ya fi dacewa da lafiyar ku, kamar yadda waɗannan sauye-sauye sun fi bayyana a cikin waɗanda suka yi barci a gefen hagu.

Duk da haka, wannan ba koren haske ba ne don daina barci gaba ɗaya a gefen hagu ba, don haka a maimakon haka, gwanda a rage kwanciya ta gefen hagu.

Ya kamata ku yi ƙoƙarin ku a ko da yaushe don guje wa barci a gefen hagu bisa ga binciken don samun lafiya.


Comments

2 responses to “Yadda bacci ta gefen hagu ke illata zuciyar mutum”

  1. […] KU KUMA KARANTA: Yadda bacci ta gefen hagu ke illata zuciyar mutum […]

  2. […] KU KUMA KARANTA: Yadda bacci ta gefen hagu ke illata zuciyar mutum […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *