Ɗan takarar shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya sake shan kaye a zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu, nasara ya kasa yi masa murmushi a wannan karon.
Atiku dai tun a shekarar 1993 ya ci gaba da sa ido a kan kujerar shugaban ƙasa amma bai samu nasara ba, inda yayi takarar shugaban jasa sau shida a shekarun 1993, 2007, 2011, 2015, 2019, da 2023, duk ya sha kayi.
Ya yi takara har sau shida domin neman tikitin takarar shugaban ƙasa, kuma a ranar 25 ga Fabrairu, shi ne karo na uku da ya fadi zaben shugaban kasa. Yana da shekaru 76, wannan na iya zama yunkurin Atiku na ƙarshe na samun gurbi a fadar shugaban ƙasa.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya fara shiga harkokin siyasa ne a shekarun 1980 a lokacin da ya yi wa Bamanga Tukur yaƙin neman zaɓen, tsohon Gwamnan tsohuwar Gongola.
KU KUMA KARANTA: Ku ƙira Tinubu, ku taya sa murna, ɗan takarar SDP ga Atiku da Obi
Ga jadawalin zaɓen shugaban ƙasa da na fidda gwani da Atiku ya yi takara kuma ya sha kaye kamar haka:
- A shekarar 1993 ya tsaya takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) wanda ya sha kaye a hannun Moshood Abiola da Baba Gana Kingibe.
- Ya kasance ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Action Congress a zaben shugaban ƙasa na 2007 ya zo na uku ga Umaru Yar’Adua na PDP da Muhammadu Buhari na ANPP.
- Ya tsaya takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaɓen shugaban ƙasa na 2011 da ya sha kaye a hannun shugaba mai ci Goodluck Jonathan.
- A shekarar 2014 ya koma jam’iyyar APC gabanin zaben shugaban ƙasa na 2015 kuma ya fafata a zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa da Muhammadu Buhari ya sha kaye.
- A shekarar 2017, ya koma jam’iyyar PDP, kuma ya kasance ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a zaɓen shugaban ƙasa na 2019, inda ya sake shan kaye a hannun shugaban ƙasa mai ci Muhammadu Buhari.
- A watan Mayun 2022, an zaɓe shi a matsayin dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaɓen 2023 bayan ya doke Nyesom Wike, gwamnan jihar Ribas a zaɓen fidda gwani. Amma ya sha kaye a hannun ɗan takarar jam’iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Tinubu.