Yadda ake tantance (Verifying) Facebook account da Facebook Page

5
1095

Daga Ibraheem El-Tafseer

Nasan kuna ganin wata alamar ‘mark’ na Good (√) mai ɗauke da kalar shuɗi (blue) a gaban sunayen wasu da yawa daga cikin manyan mutane a Facebook ko manyan Pages na Facebook irin su BBC Hausa, Daily Nigerian da sauransu. A mutane kuma akwai irinsu Rahama Abdulmajid, Sheriff Almuhajir da sauransu.

Kai tsaye kai ma za ka iya neman kamfanin na Facebook (META) da su saka maka wannan alamar a naka Account ɗin ko Page kuma su saka maka kamar yadda suka saka wa wasu.

Ga yadda abin yake, da farko za ka je setting na account ɗinka na Facebook, akwai wurin da za ka ga an rubuta ‘Help Center’ sai ka shiga wurin. Kana shiga zai buɗe maka, da zarar ya buɗe, daga can sama za ka ga akwatin yin tambaya (options), sai ka shiga wurin ka rubuta ‘How To Verify My Profile Or Page’.

Kana gama rubuta wannan, sai ka danna alamar searching, daga nan zai fara search. Yana kammala search ɗin, zai nuno maka da wani wuri da aka rubuta “You can fill out this form to verify your profile or page”. Idan ka lura da rubutun turancin za ka ga wurin da aka rubuta “fill out this form” an sanya mishi colour ɗin Blue, sai kawai ka danna wurin, kana danna wa kai tsaye zai bayyanar maka da Form ɗin da za ka cike domin miƙa musu buƙatar ka ta sanya ma Account ɗinka Blue Badge.

Ka tabbatar ka tanadi hoton Passport ɗinka ko National ID Card ko Driving license domin akwai wurin da za su buƙaci ka saka wani Identification Document naka saboda tabbatar da Account ɗin mallakinka ne. Farkon form ɗin za su tambaye ka “Profile ko Page” ne kake so ka yi Verifying ɗin? Sai ka yi ticking ɗin wanda kake so a yi maka Verifying ɗin. Kowane tsakanin Account da Page da akwai kalar Information ɗin da suke buƙata.

Akwai wani akwati da za ka gani wanda za ka saka Profile URL ko Page URL naka a wurin domin su binciki Account ko Page ɗin naka don tabbatar da ya cancanci a yi verifying ɗinsa ko bai cancanta ba.

KU KUMA KARANTA: Gwamnatin Najeriya ta yi ƙarar kamfanin Facebook tana neman ya biya tarar N30bn

Bayan ka gama cike form ɗin daga ƙarshen form ɗin akwai wurin da za ka yi Submitting, kana gama wa shikenan, za ka ga sun dawo da kai baya, alamun buƙatarka ta tafi, dan haka za su yi bincike a kan Page ɗin ko Account ɗin naka zuwa wani lokaci da zaran sun kammala suka tabbatar babu wasu Restrictions a account ɗin naka to za ka ga sun yi Verifying account ɗinka. Idan kuma akwai wani Restrictions to lallai sai account ɗinka ya fita daga restrictions nasu sannan za su yi Verifying ɗinsa.

Sannan idan ka yi Requesting sau ɗaya ka ga an daɗe ba su turo maka wani saƙo ba kuma ba suyi verifying ɗinka ba, za ka iya ƙara cike form exactly kamar yadda ka cike a baya ka sake tura musu.

5 COMMENTS

Leave a Reply