Amfanin manhajar Gmail a wayoyin hannu

0
289

Daga Ibraheem El-Tafseer

Amfanin Manhajar Gmail A Wayoyin Hannu
Manhajar Gmail ɗaya ne daga cikin ’email service provider’ da kamfanin Google ke gudanar da shi. Ga mai amfani da wayar Android ‘email’ na kamfanin Google (Gmail) zai fi yi masa amfani fiye da sauran ‘providers’ irinsu Yahoo, Hotmail, Yanded, outlook da sauransu.

Da yawan mutane in an ce Google, sukan taƙaita shi da ‘searching engine’ ma’ana wurin da za ka yi browsing (bincike) na wani abu, in kuma aka ambaci ‘Gmail’, da yawa mukan taƙaita aikinsa da turawa ko karɓar saƙon ‘email’ da ajiye lambar waya, amma duk amfaninsa ya wuce nan.

Google shi ne kamfanin da yafi kowane kamfani ƙarfi a duniyar fasahar sadarwa. Shi ne kamfani da yake gudanar da OS (operating system) na Android tare da shi da sauran wasu kamfanoni. Android shi ne OS da mafi yawancinmu muka fi amfani da shi a wayoyinmu na Samsung, Pidel, Tecno, Infinid, Itel, Diomi, Gionee, Huawei, HTC, Motorola, Oppo, Nokia, Bibo da sauransu.

Idan ka buɗe ‘Gmail Account’ kai tsaye ka yi rijista ne ‘Google account and services’, ma’ana za ka yi amfani da duk wani tsare-tsare da manhajoji 131 da Google ke gudanar da su (about.google/products), waɗanda iya mai Google account ne kaɗai zai iya morarsu kai tsaye ɗari bisa ɗari.

KU KUMA KARANTA: Yadda ake tantance (Verifying) Facebook account da Facebook Page

Waɗannan manhajojin sun haɗa da Gmail, Playstore, YouTube, Google Drive, Photos, Blogger, Forms, Alerts, AdSense, Google Chats, Google classroom, Family Link, Find My Device, Google Groups, Contacts, Message, Google one, Podcast, Hangouts, Scholar, Meet, AdMob, Cloud, Translate… da sauransu. Kuma ana amfani da su wajen tura saƙonni, karatu, kasuwanci, developing, taruka, adana bayanai, ƙididdiga da sauransu.

Mallakar ‘Google account’ yana taimaka wa wajen Auto-Fill na Login Credentials (bayanai da za ka shiga domin buɗe wani shafi, wato (username da password); ma’ana, idan ka yi saving bayanan shiga wani shafi (kamar Facebook ko Twitter), babu buƙatar sai ka yi typing na ‘username da password’, a’a kai tsaye Auto-Fill zai shigar maka da bayanan.

Ba za mu iya bayanin dukkan ‘Manhajoji 131′ ba a yanzu, ba kuma lalle a ce sai ka iya amfani da dukkanin manhajojin ba (ya danganta da wanda kake buƙatar amfani da shi), sannan wasun su ba a iya amfani da su a wasu ƙasashen.

Ga bayanin wasu atakaice:

PLAYSTORE– Rumbu ne mai ɗauke da manhajojin Android (apk) 2.59 million (Statista, 2022). Mai Google account (Gmail) ne kaɗai zai iya shiga domin sauƙe ‘apps’ daga cikin Play store.

KU KUMA KARANTA: Yadda za ka kare shafinka na Facebook da Twitter daga masu ƙwace

GOOGLE CONTACTS – ‘App’ ne da ake iya adana lambobin waya daga 1 zuwa 25,000. Amfani da ‘Google Contact’ na da matuƙar muhimmanci, saboda ko an sami akasi wayarka ta ɓata, ko lalace, ko aka sace, da zarar ka sami wata wayar ko a computer za ka iya dawo da duk ‘lambobin wayarka’ da ka adana (saving) a cikinsa.

BLOGGER– zaka iya ƙirƙirar ‘blog site’ da Blogger, har kana iya wallafa rubutu kyauta. Idan kana samun traffic da yawa, za ka iya ‘rijista’ da ‘AdSense’ ka fara samun kuɗin da Blogger ɗin, musamman idan kana ɗora talla/ads (misali, neptuneprime.blogspot.com)

FIND MY DEVICE – manhaja ce da za ta taimaka wajen gano inda wayarka take, idan ka rasa ta, ko ka jefar, ko aka sace.

YOUTUBE – wannan sananne ‘app’ ne na Google da za ka iya buɗe ‘channel’ da shi ta hanyar amfani da ‘Google Account’. Idan kana samun traffic da yawa, aƙalla subscribers 1000. kuma aka samu an buɗe ‘contents’ na ka kamar sau 4000, za ka iya fara samun kuɗi da YouTube.

GOOGLE PHOTOS – Wannan manhajar tana taimaka wa sosai wajen adana hotunan cikin waya. Idan kana ‘backup’ na hotuna a cikin ‘Photos’ za a iya ‘restoring’ nasu a kowace irin waya ka canza, a kowane lokaci.

GOOGLE DRIVE – wannan manhajar ‘cloud’ ce da ke iya bawa mutum damar ajiye ‘files’ a ciki. Suna bawa kowane user (mutum) ‘storage’ na 15 gigabytes. Za ka iya buɗe abubuwa da ka adana a cikin Drive a kowace waya ko computer idan ka yi amfani da ‘Google Account’ (Gmail) naka.

SCHOLAR – Google scholar kamar ‘Google searching engine’ ne. Yana taimaka wa wajen lalubo metadata (ta rubuce-rubuce na ilimi).

Misali, idan ka sami wani rubutu, kuma kana son ba shi ‘reference’ idan ka ɗauki ‘jumla’ ka ɗora a scholar zai ba ka irin wannan jumlar ta bayyana a rubuce-rubuce da suka gabata, cikin littattafai, ko muƙala (articles), ko journals, ko mujalla da sauransu.

CHROME REMOTE DESKTOP – manhaja ce da za ta ba ka damar shiga cikin files na computer daga wayarka, ko da ba ka tare da computer ɗin.

KU KUMA KARANTA: Anya Facebook dandalin sada zumunta ne kuwa? (I)

GOOGLE ADS – Manhajar AdSense da AdMob na taimaka wa masu amfani a social media yin rijista domin samun kuɗi ta hanyar ɗora talla a shafukansu (ads).

MEETS – Kamar zoom yake, ana iya yin meeting online.

Akwai sauran apps na Google da za su taimaka sosai wajen developing, kamar optimize, Google Analytics, Google Cloud, Firebase, Flutter, Play Protect, Play Games, Survey, Web da sauransu.

Akwai apps na Google da za su taimaka wajen editing na hoto, SNAP SEED da PHOTOS. Akwai na duba taswira (map), GOOGLE MAP da GOOGLE EARTH. Akwai manhajar karɓar bayanai ta GOOGLE FORMS, akwai manhajar fassara ta TRANSLATE. Akwai manhajoji da yawa na GOOGLE, sai a hankali ko in buƙata ta tashi, za mu ɗauki wasu muna bayaninsu a taƙaice.

Yawancin waɗancan tsare-tsare na Google, iya masu Google account (Gmail) ke iya morarsu sosai. Ana iya amfani da Gmail, kamar sauran ‘providers’ (Yahoo, Hotmail…) wajen yin rijista ko cike-ciken da ake yi a yanar gizo, kamar buɗe profile na makaranta ko cike aiki (job application), ko cike tallafi, misalin, survival fund da sauran cike-cike. Kar ka yi gangancin ba wa kowa Login details na Gmail naka, domin za a iya shiga (accessing) dukkan waɗancan tsare-tsaren da shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here