Yadda Abba Kabir Yusuf na NNPP ya lashe zaɓen Kano

3
395

Hukumar INEC ta bayyana Abba Kabir Yusuf na NNPP a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan Kano.

Hukumar Zaɓen mai zaman kanta ta Ƙasa ta bayyana ɗan takarar jam’iyyar NNPP Abba Kabir Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Kano da sanyin safiyar Litinin.

KU KUMA KARANTA: Jam’iyyun APC da NNPP sun umurci magoya bayansu da su tare a cibiyoyin tattara zaɓe a Kano

Abba ya doke babban abokin hamayyarsa na jam’iyyar APC, Nasiru Yusuf Gawuna, inda ya yi nasara da ƙuri’u 1,190 602 yayin da Gawuna ke biye masa da kuri’u 890,705.

Yanzu haka dai mutanen birnin Kano sun fara bayyana murnarsu bayan samun sakamakon.

3 COMMENTS

Leave a Reply