Tsohon jami’in rundunar kwastam, ACG Kamilu Ado ya rasu ana saura kwanaki shida zaɓe a Kano, sai ɗan takarar shugaban Ƙasa na jam’iyyar NNPP, Dokat Rabiu Musa Kwankwaso ya ce a bawa ɗan Marigayin takarar bayan mahaifinsa ya rasu, cikin ikon Allah sai ya lashe zaɓen Ɗan Majalisar Tarayya Mai wakiltar ƙananan hukumomin Wudil da Garko.
Abubuwan da ya kamata ku sani game da ɗan da ya gaji takarar mahaifinsa, Sheikh Abdul Hakeem Kamilu Ado
Sunan sa Shekh Abdulhakeem Kamilu Ado Wudil, yana da Shekaru 30,Bayan Mutuwar Mahaifinsa kwana shida ga zaɓe jam’iyyar NNPP ta bashi takarar saboda nagartarsa.
KU KUMA KARANTA: Yadda yaro ɗan shekara 20 ya sace mahaifiyarsa, ya karɓi kuɗin fansa naira miliyan 30 a Zamfara
Ya kasance mahaddacin Alqur’ani
Makarancin hadith da Fiqh.
Yayi karatun digirinsa na farko a jami’ar ABU Zaria, kuma yanzu haka yana karatun digirinsa na biyu a jami’ar.
Malamin jami’a ne a jami’ar Al-Istiqama da ke Sumaila a Kano.
Yana da cibiyar koyarwa wato Markaz ta koyarwar addini a masallacin jami’ar KUST da ke Wudil da kuma sauran majalisai.