No menu items!

Sample Page Title

Date:

Ya zama wajibi Najeriya ta samu nasarar yaƙi da ‘yan ta’adda — Hafsan Sojojin Ƙasa

Daga Jameel Lawan Yakasai

Babban Hafsan Sojin Kasa, Laftanar-Janar Olufemi Oluyede, ya bayyana cewa nasarar Najeriya kan ‘yan ta’adda da dukkan makiyan kasa tabbas ce.

Janar Oluyede ya sake jaddada kudirin rundunar sojin Najeriya na kawar da ta’addanci tare da tabbatar da tsaron kasa ta hanyar dabarun yaki da ta’addanci masu inganci.

Ya fadi hakan ne a yayin bikin addu’ar cocin addinai daban-daban da aka gudanar domin bikin ranar rundunar sojin kasa ta Najeriya na shekarar 2025 a ranar Lahadi a birnin Abuja.

KU KUMA KARANTA: Gwamna Yobe ya ziyarci sansanin soji da ke Buni Gari, ya tallafawa iyalan Sojojin da aka kashe

Ya kara da cewa sojin Najeriya ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen kare ikon kasa da kuma kare ‘yancin dukkan ‘yan Najeriya.

“Ba za mu taba barin darajar mu ba, wacce ke da nasaba da bangaskiyarmu, kuma za mu ci gaba da rayuwa bisa taken rundunar sojin Najeriya wato: ‘Nasara daga Allah kadai take.”

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...