Gwamna Yobe ya ziyarci sansanin soji da ke Buni Gari, ya tallafawa iyalan Sojojin da aka kashe

0
63
Gwamna Yobe ya ziyarci sansanin soji da ke Buni Gari, ya tallafawa iyalan Sojojin da aka kashe

Gwamna Yobe ya ziyarci sansanin soji da ke Buni Gari, ya tallafawa iyalan Sojojin da aka kashe

Daga Ibraheem El-Tafseer

Gwamnan jihar Yobe Hon. Mai Mala Buni, a yau Alhamis, ya ziyarci Hedikwatar Soji ta ’27 Task Force Brigade Buni Gari’, domin jajantawa waɗanda aka kashe a harin da ‘yan tada ƙayar baya suka kai sansanin.

Gwamna Buni ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici game da sake ɓullar tashe-tashen hankula da kuma hare-haren da ake kaiwa jami’an tsaro.

Gwamnan ya jajanta wa sojoji da iyalan ma’aikatan da suka mutu, yana mai cewa, “Jami’an ba su mutu a banza ba, sun mutu ne suna kare ƙasarsu”.

KU KUMA KARANTA: Gwamnan Yobe ya ziyarci aikin magudanar ruwa a Damaturu

Gwamnan ya bayar da tallafin Naira Miliyan 2 ga kowane ɗaya daga cikin iyalan jaruman sojojin da suka mutu, sannan kuma ya ba da Naira miliyan 1 ga duk wanda ya samu rauni.

Buni ya ce gwamnati za ta kuma bayar da tallafin ilimi ga yaran sojojin da suka mutu.

Hakazalika, Gwamnan ya sanar da bayar da gudunmuwar Naira miliyan 50 da za a raba wa dakarun rundunar ta 27 Brigade Buni Gari, ba ya ga kayan abinci, katifa, barguna, da sauran kayayyaki da gwamnatin jihar ta bayar.


Ya kuma ba da tabbacin goyon bayan gwamnati da al’ummar jihar ga sojoji da sauran jami’an tsaro domin yaƙar su yadda ya kamata tare da fatattakarsu.

Gwamna Buni ya ba da umarnin ƙarfafa tsaro a kewayen Birgediya, inda ya ba da tabbacin goyon bayan gwamnati ga jami’an tsaro “Za mu ci gaba da ƙara ƙaimi wajen inganta tsaro a kusa da kafaku”.

Kwamandan Birgediya Janar Usman Ahmed, wanda ya jagoranci Gwamnan wajen kafa wannan ƙungiya, ya yabawa Gwamna Buni kan yadda ba a saba nuna damuwa da kulawa ga sojoji ba.

Leave a Reply