Wani ɗan kasuwa mai suna Raphael Chima ya maka matarsa Joy a gaban wata kotun gargajiya da ke Jikwoyi, Abuja, babban birnin tarayya Abuja, saboda yadda take yawan marinsa har da duka.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, (NAN), ta ruwaito cewa Raphael ya yi wannan zargin ne a cikin takardar neman saki da ya shigar da Joy a gaban kotu.
“Matata tana cin zarafi da tsangwama na. Ta na mari na a ko da yaushe, da ta samu dama ko kaɗan ne. Ga zagi na,” inji shi.
Ya kuma shaida wa kotun cewa matarsa ta raina iyayensa. Mai shigar da ƙarar ya shaida wa kotun cewa matarsa ta daɗe da barin ɗansu ɗaya tilo, kuma shi ne ke kula da shi.
KU KUMA KARANTA: Miji ya saki matarsa bayan ta nemo masa kuɗin zuwa Saudiya
Ya roƙi kotu da ta raba auren da ke tsakaninsa da matarsa, ta kuma ba shi riƙon yaron nasu.
Wanda ake ƙara, Joy ta musanta zargin. Alƙalin kotun, Dada Oluwaseyi, ya shawarci ma’auratan da su sulhunta kansu.
Oluwaseyi ya ɗage ci gaba da sauraron ƙarar domin samun rahoton sasantawa ko kuma sauraron ƙarar.
[…] KU KUMA KARANTA: Ya maka matarsa a kotu, saboda tana yawan marinsa […]
[…] KU KUMA KARANTA: Ya maka matarsa a kotu, saboda tana yawan marinsa […]