A ranar talata ne hukumar Hisbah ta jihar Kano ta yi watsi da rashin fahimtar da matar da ta auri tsohon mai neman ‘yarta yayi a ƙaramar hukumar Rano a jihar Kano.
Matar mai suna Malama Khadija ta raba aurenta kuma ta auri saurayin ɗiyarta, lamarin ya faru ne bayan ɗiyar matar mai suna A’isha ta ƙi amincewa da tsohon saurayin nata, lamarin da ya haifar da cece-kuce a sakamakon haka hukumar Hisbah ta kafa wani kwamiti da zai binciki lamarin.
Kwamitin da ya binciki ce-ce-ku-ce a kan auren, ya miƙa rahotonsa da yammacin ranar Talata, da yake gabatar da rahoton, shugaban kwamitin wanda ya zama mataimakin kwamanda mai kula da ayyuka na musamman na Hisbah, Hussain Ahmed, ya bayyana cewa kwamitin ya gano cewa auren ya dace kuma ya cika dukkan sharruɗan da suka dace.
Ya bayyana cewa matar mai suna Khadija Rano, tsohon mijinta ne ya sake ta, kuma ta cika watanni uku (iddah) da Musulunci ya tsara, kuma daga baya ta auri wani mutum da ɗiyarta ta ƙi yarda da shi a baya.
KU KUMA KARANTA:‘Ta kashe aurenta don ta auri tsohon saurayin ‘yarta’
Ahmed ya yi watsi da raɗe-raɗin da ake yaɗawa cewa Khadijah tana ganin sabon mijin nata tana aure kuma ta ingiza mijinta ya sake ta domin ta auri mai neman ɗiyarta.
Ya kuma bayyana cewa auren ya halasta bisa addinin Musulunci, inda ya ce dalilin da ya sa kwamandan Hisbah na ƙaramar hukumar Rano ya goyi bayan da kuma halartar bikin aure.
Da yake mayar da martani babban kwamandan hukumar Hisbah Sheikh Harun Ibn Sina ya yabawa kwamitin bisa gudanar da ayyukansa yadda ya kamata, ya ce an zaɓo ‘yan kwamitin ne cikin tsanaki, saboda ɗimbin ilimin da suke da shi na koyarwar addinin Musulunci da fahimtar al’umma.
Ibn Sina ya ja kunnen jama’a da su guji yaɗa labaran ƙarya da kuma nisantar rashin fahimta kan al’amuran da suka shafi Musulunci, ya kuma shawarce su da su nemi ilimi, kasancewar Musulunci addini ne da ya kebe hukunce-hukuncen aure, da rayuwar iyali da duk wani abin da ya shafi rayuwar ɗan Adam.
A makon da ya gabata ne kafafen sada zumunta suka cika da rahotanni game da matar da ake zargin ta kashe aurenta domin auran saurayin ɗiyarta.