WHO za ta aike da tawaga ta musamman Rwanda bayan ɓullar cutar Marburg

0
39
WHO za ta aike da tawaga ta musamman Rwanda bayan ɓullar cutar Marburg

WHO za ta aike da tawaga ta musamman Rwanda bayan ɓullar cutar Marburg

Hukumar WHO na duba yiwuwar aikewa da tawaga ta musamman zuwa Rwanda bayan yaɗuwar annobar cutar Marburg da kawo yanzu ta hallaka mutane aƙalla 7, galibinsu jami’an lafiya baya ga gano ta a jikin mutane fiye da 26.

Shugabar hukumar ta WHO shiyyar Afrika Dr Matshidiso Moeti ta bayyana cewa nan kusa za ta aike da tawagar ƙwararrun jami’ai zuwa ƙasar ta Rwanda daga ofishinta da ke Kenya.

Ma’aikatar lafiyar Rwanda ta ce tuni ta bi diddigin kusan dukkanin mutanen 121 da suka yi mu’amala da waɗanda cutar ta kashe inda yanzu haka aka killace su a wani yunƙuri na daƙile barazanar cutar mai haɗari.

Cutar ta Marburg da ke cikin dangin Ebola, na sahun cutukan da wasu kan yaɗawa wasu ta hanyar mu’amalar da ta ƙunshi ko dai musabaha da za ta kai ga shafar jiki ko kuma musayar lumfashi.

KU KUMA KARANTA: Fiye da mutum miliyan bakwai ke kamuwa da cutar shanyewar ɓarin jiki duk shekara – Bincike

Masana kiwon lafiya na bayar da shawarwarin killace dukkanin wanda ake fargabar ya kamu da wannan cuta don daƙile barazanar yaɗuwarta.

Zuwa yanzu cutar ta fantsama zuwa sassa 7 cikin yankuna 30 na Rwanda ciki har da Kigali fadar gwamnatin ƙasar.

Leave a Reply