Watanni biyu da aurensu, ta roƙi kotu da ta raba auren

5
500

Bayan ɗaurin aurensu da wata biyu kacal, wata matar aure mai suna Salamatu Suleiman, ta shigar da ƙara kotu akan a raba auren, saboda rashin lafiyar mijinta.

Mai shigar da ƙarar ta shaida wa kotun cewa ta lura maniyyin mijin na ta ba shi da kauri.

Ta roƙi kotu da ta raba auren, inda ta ce ta gaji da auren.

Wanda ake ƙara ya yarda cewa yana da matsalar lafiya, amma ya dage cewa matar ma tana da ƙalubalen lafiya ita ma.

Sai dai ya ce har yanzu yana son matarsa ​​kuma ya roƙi kotu da ta ba shi lokaci domin ya sasanta rikicin.

KU KUMA KARANTA: Matata ta auri wani mutum a asirce – miji ya shaida wa kotu

Alƙalin kotun mai shari’a Abdulƙadir Umar ya shaida wa uwargidan da ta kasance da hankali da kuma neman agajin lafiya a kan ƙalubalen da suke fuskanta.

Alƙalin ya shawarci matar da ta ba da dama ta biyu a zamantakewar su, inda ya nuna cewa duk aure yana da ƙalubale.

Kotun ta ɗage sauraren ƙarar zuwa ranar 28 ga watan Agusta, domin samun rahoton sasantawa ko kuma ci gaba da sauraron ƙarar.

5 COMMENTS

Leave a Reply