Wata mata ta ciji al’aurar sirikin ta

0
290

Wani dattijo mai shekaru 78 a mazabar Bumula da ke gundumar Bungoma ta Kenya, yana fama da raunuka a al’aurarsa bayan da aka yi zargin surukarsa ta yi masa awata hatsaniya.

A kokarin da ake na sasanta rikicin da ya ɓarke tsakanin matar da kawarta a gidansu da ke ƙaramar hukumar Kimaeti a ranar Asabar, 28 ga watan Janairu, 2023, an ce Evelyn Okello, matar dansa ta biyu ce ta kai wa Vincent Barasa hari.

Da yake magana da Citizen TV Kenya a ranar talata 31 ga Janairu, Barasa ya ce yana cin abinci da misalin karfe 4 na yamma sai ya ji hayaniya a gidan ɗansa Godfrey Wekesa.

KU KUMA KARANTA:Wasu fusatattun mata su 8 sunyiwa matar aure duka a Jihar Kano

Ɗaya daga cikin jikokinsa ya sanar da shi cewa surukarsa na faɗa da wata mace daga wata kasuwa da ke kusa. Nan da nan ya garzaya wurin da lamarin ya faru a kokarinsa na sasanta rikicin amma ya ci karo da shi inda ya yanke shawarar komawa baya ba tare da wani kokari ba.

Bai daɗe da komawa ba, Evelyn ta bi shi ta buge shi da dutse. Ya faɗi a sume, matar ta zauna masa a kirji tana cizon shi. Kokarin da dattijon ya yi na ture ta ya ci tura, sai ta koma ta cije al’aurarsa.

“Lokacin da nake komawa, ga alama matar ta fusata don haka ta jefe ni da dutse ta bugi bayan kaina. Sai ta ci gaba da cizon al’aura ta.” ya bayyana.

Bayan afkuwar lamarin, fusatattun mazauna wurin da suka isa wurin sun yi wa matar da mijinta dukan tsiya kafin su ɗauki dattijon domin yi musu magani.

Wekesa ya ce matarsa ​​tana yawan samun tashin hankali kuma sau da yawa tana zargin cewa za ta kashe shi da ɗiyarsa.

A halin da ake ciki dai, ‘yan sanda na ci gaba da zakulo wanda ake zargin wanda tuni ta ɓuya.

Leave a Reply