Wata fashewa daga wata ma’adanar mai da ake zargin ba bisa ka’ida ba a Kano a ranar Litinin, 8 ga watan Janairu, ya kashe mutum ɗaya, ya ƙona aƙalla gidaje biyar da wata babbar mota.
Lamarin ya faru ne a unguwar Katango General dake Wailari, ta hanyar Western Bypass, daura da gidan Maryam Shekarau, dake kan titin Ring, Kano.
Kimanin sa’o’i uku aka kwashe tare da haɗin gwiwar jami’an hukumar kashe gobara ta jihar Kano da hukumar bada agajin gaggawa ta ƙasa NEMA da ma’aikatan kashe gobara daga gidan man Salbas wajen shawo kan gobarar.
Wani direban babbar motar da ake ƙira Aminu da ke cikin matatar man, ya ƙone ƙurmus ba a iya gane shi.
KU KUMA KARANTA: Gobara ta cinye ɗaruruwan shaguna a kasuwar Gwarzo
Jami’an hukumar kashe gobara sun gano gawar sa, yayin suka isa wurin da lamarin ya faru bayan isarsu Wajen.
“Gidaje biyar sun kona da ƙurmus sakamakon gobarar da ta girgiza mazauna unguwar,” in ji wani ganau.
An ceto wata tsohuwa da ta ƙasa tafiya daga ɗaya daga cikin gidajen. Haka kuma, an ceto wasu yara biyu daga wani gida, wanda mahaifiyarsu ta fita a guje ta bar su a ciki.
Ahmad Umar Gaya, ma’aikacin ofishin duba ababen hawa (VIO), ya shaida wa manema labarai cewa, yana bakin hanya ne ya ji ƙarar fashewar wani abu.
“Wurin, wanda ke tsakiyar gidajen zama a Katango a Wailari, ana amfani da shi ne wajen adana tarkacen manyan motoci da tireloli da kuma tace man injin da aka yi amfani da shi don wasu dalilai.
“Babu wanda zai iya bayyana ainihin abin da ya faru wanda ya kai ga fashewar. Tirelar da ke ɗauke da ganguna na man inji da ake yi amfani da su ta ƙone sakamakon gobarar, shima direban ya ƙone ƙurmus.
“A kusa da wurin akwai gidaje da mata da yara, kuma kusan gidaje biyar ne gobara ta ƙone.”