Wasu daga cikin amfanin ‘ya’yan magarya da ganyenta

0
310

A turance ana ƙiranta “Ziziphus abyssinica”.
Tarihi ya nuna an fara amfani da MAGARYA da kuma ganyenta tun kafin zuwan Addinin musulunci. A Larabce ana ƙiran itacen magarya “ASSIDIR” bayan zuwan addinin musulunci malamai da masana magunguna suka ba da fatawar cewa za a iya amfani da magarya domin magance da yawa daga cikin cututukkan yau da kullum.

Haka yake wajen turawa sunyi iya binciken su ba su ƙididdige alfanun magarya ba, sai dai suka kawo kaɗan daga abin da suka sani, domin sau da yawa dama maganin da bature ke amfani da shi itacen mune wasu ma a yankunan turawan babu su mu kuma cikin tausayi na ubangiji sai ya bamu amma kuma mun daƙile kanmu wajen sanin alfanunsu.

KU KUMA KARANTA: Ko kasan amfani da illolin Tumatir?

Ba dogon bayani zan yi akan itacen magarya ba illa dai zan kawo wasu daga alfanunsa da kuma yadda ake sarrafasu zuwa magani.

  1. Ganyen magarya yana tsaftace jini domin yana ɗauke da sinadarin kashe ƙwayoyin cuta masu shiga jiki musamman mace lokacin da tagama al’ada (menstruation) wannan yasa ake son mace lokacin da ta gama al’ada ta tafasa ganyen magarya tana tsarki da ruwan aƙalla kwanaki 3 a jare.
  2. Garin magarya kuwa mace ko namiji za su iya amfani da shi suna sha a nono domin magance matsalar gyambon ciki wato (ulcer).
  3. Domin magance matsalar sanyi na mata (infection) musamman zubar ruwa a gaban mace sanadin wannan sanyin a samu ganyen zogale, bagaruwar hausa, sauyar zogale, a haɗa da kanamfari a tafasa ana zama acikin ruwan. Amma banda budurwa.

Leave a Reply