No menu items!

Sample Page Title

Date:

Wani ɗan Kenya ya cinna wa kansa wuta saboda tsadar rayuwa a birnin Mombasa na ƙasar.

Tun da farko dai mutumin ya ce yana zanga-zanga kan tsadar, kafin daga bisani ya cinna wa kansa wuta a ranar Alhamis da tsakar rana.

Ya hau kan wani wurin mutum-mutumi da ke tsakiyar wani shatale-tale kafin cinna wutar.

Wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta, ya nuna mutumin riƙe da tutar ƙasar ta Kenya yana ihu, inda nan da nan kawai sai aka ga wuta ta turnuke wajen.

Wasu mutane da ke wucewa ne suka taimaka wajen kashe wutar tare da garzaya da mutumin wani Asibiti da ke kusa, inda ake yi masa jinya.

KU KUMA KARANTA: Ƴan bindiga sun kashe basarake sun ƙona gawarsa a Imo

Shaidu sun ce mutumin wanda ba a bayyana sunansa ba, na zanga-zanga ne kan tsadar rayuwa da kuma tafka maguɗi a zaɓen shugaban ƙasa da ya gabata, wanda madugun adawar ƙasar Raila Odinga ya sha kaye a hannun Shugaba Wlliam Ruto.

Kotu dai ta tabbatar da nasarar Ruto sannan ta kori ƙarar Mista Odinga wanda ya ce an aikata ba daidai ba a zaɓen.

An kashe dubban mutane a Kenya a baya-bayan nan yayin da ‘yan sanda suka far wa masu zanga-zanga da ke neman a yi wa ɓangaren zaɓen ƙasar garanbawul da kuma kawo ƙarshen tsadar kayayyaki.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...