Wani ya ƙone budurwa saboda ta ƙi auren shi

0
57
Wani ya ƙone budurwa saboda ta ƙi auren shi

Wani ya ƙone budurwa saboda ta ƙi auren shi

An gurfanar da wani mutum mai suna Abdullahi Idris, a gaban kotun shari’ar Musulunci a Jihar Kano, saboda zargin ƙone budurwarsa, Sa’adatu Ibrahim, saboda ta ƙi amincewa da aurensa.

Idris, wanda yake zaune a garin Rimi, ƙaramar hukumar Sumaila, ya kasance yana soyayya da Sa’adatu, wadda bazawara ce.

Ya shafe tsawon kwanaki bakwai yana muradin ta amince da batun aurensa amma ta ƙi amincewa da buƙatar tayin da ya mata.

KU KUMA KARANTA: Gobara ta cinye ɗaruruwan shaguna a kasuwar Gwarzo

An tuhume shi da laifin yin sharri, ƙone mutum, da yunƙurin kisan kai, sai dai duk da haka ya musanta dukkanin tuhume-tuhumen da ake masa.

Lauyan mai shigar da ƙara, Barrista Maryam Jubril, ta nemi a ɗage shari’ar zuwa wani lokaci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here