Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta cafke wani da ake zargi da aikata kisan kai, mai suna Usman Yahaya Muhammed, wanda ya kashe wani ɗan achaɓa tare da sace babur ɗinsa a ƙaramar hukumar Mokwa da ke jihar.
Wanda ake zargin, wanda ɗan banga ne na yankin, ya kashe ɗan acaɓan ne ranar Juma’a, 29 ga Satumba, 2023, ya saci babur ɗin da nufin ya sayar da shi kuma ya tara kuɗi don bikin aurensa.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Wasiu Abiodun ya gabatar da wanda ake zargin a ranar Litinin, 9 ga watan Oktoba, tare da wasu da aka kama bisa laifuka daban-daban a jihar.
“A ranar 1/10/2023 da misalin ƙarfe 08:30, an samu labarin cewa an tsinci gawa wanda aka yankewa makogwaro jina-jina a unguwar Shabalile da ke Mokwa. Jami’an ‘yan sanda ƙarƙashin jagorancin DPO reshen Mokwa sun ke wurin da lamarin ya faru inda suka ɗauki gawar zuwa ɗakin ajiye gawa na Asibiti,” in ji PPRO.
“A binciken da ake yi a ranar 2/10/2023 da misalin ƙarfe 11:30, an gano wani babur Bajaj da ake zargin an yi wa mamacin fashi ne a wani gini da ba a kammala ba a Mokwa, yayin da bincike ya kai ga kama wani Usman Yahaya Muhammed mai shekara 20 na ƙauyen Kinboku-Kudu a Mokwa.
KU KUMA KARANTA: Wasu mutane a Lokoja, sun kashe wata mata da duka a tashar mota
“Lokacin da ake yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya amsa laifinsa kuma ya ce ya hau babur ɗin zuwa ƙauyen Eppa, kuma a kan hanyar su ne ya tsayar da mahayin ya yi masa sare shi har lahira. Ya jefar da gawar ya tafi da babur. Ana binciken lamarin a SCID Minna.”
Da yake magana da manema labarai, wanda ake zargin ya ce an shirya ɗaurin auren nasa ne ranar Juma’a sannan kuma ya amsa laifin aikata irin wadannan laifuka sau takwas a baya.