Daga Ibraheem El-Tafseer
Sha ko tsotsan ɗan yatsan hannu, wanda a turance ake ƙira da “thumb sucking” abu ne wanda mafiya yawa ake samun ƙananan yara da shi, sai dai yana raguwa da zarar yaro ya haura sama da wata shida da haihuwa. Sai dai mafiya yawan yara suna ci gaba da shan ɗan yatsa duk da sun haura sama da shekara biyu zuwa sama da haihuwa, domin yin hakan yana sa su ji daɗi da kuma ɗauke musu kewa da ɓacin rai.
Shan ɗan yatsa kan iya zama halayya (habits) a ƙananan yara da kuma jarirai waɗanda suke yin hakan don gamsar da kansu a lokacin da suke jin yunwa, bacci, tsoro, gajiya da kuma zama shiru.
GA WASU DAGA CIKIN ABUBUWA DA SHAN ƊAN YATSA KE HAIFARWA
Shan ɗan yatsan hannu kan iya haifar da matsaloli da dama, musamman ma waɗanda suka haura shekara biyar zuwa sama. Matsalolin sune kamar haka :
1: Karkacewan haƙora (Malocclusion) wanda hakan ke sa haƙora na gaba ka ga sun yi kamar za su fito waje (protrude) ko kuma ka ga ba sa haɗuwa da juna ko ka kulle baki (open bite) da dai sauransu.
KU KUMA KARANTA: Ko kasan maganin ciwon haƙori sadidan?
2: Shan ɗan yatsa zai iya haifar da gura-gura (lisping) saboda tazarar (space) da ake samu tsakanin haƙora na sama da ƙasa (open bite), saboda daɗewa da aka yi ana shan ɗan yatsan.
3: Shan ɗan yatsa kan iya saka muƙamuƙi (Jaw) ya canza daga yadda siffarsa take zuwa faɗi, saboda ƙarfi da ake saka masa yayin tsosan yatsa.
4: Shan ɗan yatsa kan iya kawo hangula da kumburi a dadashi (gum) da wasu cututtuka da ya danganci dadashi.
Masani a wannan fanni, Rdst Ayuba Musa ne ya bayyana haka, sai dai ya ce, waɗannan na daga cikin abubuwan da sha ko tsotsan ɗan yatsa ke haifarwa, sai dai idan aka yi sa’a yaro ya daina shan ɗan yatsa tun kafin haƙoran shi na shayarwa wato “Milk Teeth” su faɗi toh duk waɗannan abubuwan da na lissafo ba za su faru ba insha Allah.