Ɗan ƙasar China mai suna Frank Geng-Quangrong mai shekaru 47 a duniya da ake tuhuma da kisan budurwarsa a Kano, ya sake gurfanar a koto a ranar Laraba 11 ga watan Junairun 2023 inda ya shaidawa wata babbar kotun jihar Kano cewa ya kashe sama da naira miliyan 60 akan budurwar tasa Ummukulsum Sani.
Idan baku manta ba, gwamnatin jihar Kano na gurfanar da wanda ake zargi da kashe budurwar tasa ‘yar shekara 23 bayan an zarge shi daɓa mata wuƙa lamarin da ya yi sanadiyar mutuwarta a unguwar Janbulo a Kano. Kano bayan wata hatsaniya.
A ci gaba da shari’ar a gaban mai shari’a Sanusi Ado Ma’aji na babbar kotun Kano a ranar Laraba, wanda ake zargin ya bayyana wa kotu yadda marigayiya Ummukulsum ta karya zuciyarsa har sau biyu kan alƙawarin auren da ta yi masa.
KU KUMA KARANTA:Mr Geng ya musanta zargin kashe Ummita a Kano
“A watan Yuni 2020 Ummukulsum ta sami lambar wayata daga wajen ƙawarta ta kira ni, ta shaida min tana sona, kuma da yardar Allah za ta aure ni.
“Mun fara dangantakarmu a watan Yulin 2020 kuma ta fara neman na bata kuɗi, na kuma ba ta duk abin da take so saboda ina sonta.
“Na tura mata sama da naira miliyan 60 zuwa asusun ajiyarta na bankin GT, naira miliyan 18 don fara kasuwanci, da kuma gidan naira miliyan 4 da naira miliyan 6 na tallafin karatunta a Jami’a da dai sauransu.
“Duk lokacin da na je na ɗaukar ta don cin abincin dare a gidan mahaifiyarta ko yaushe tana maraba da ni hannu biyu-biyu,” in ji shi.
Frank ya shaidawa kotun cewa a watan Fabrairun 2022, marigayiyar ta auri wani.
“Na ji takaici sossai don haka na koma Abuja.
“Ta ci gaba da ƙirana tana hira da ni ta Whatsapp ta ci gaba da neman kuɗi a waje na.
“Daga baya Ummukulsum ta gaya mani cewa sun rabu da mijinta, ta nemi in dawo wurinta, ta kuma yi min alƙawarin aure na a karo na biyu.
Ya ce a ranar 13 ga Satumba, 2022 Ummukulsum ta nemi kuɗi domin ta ci gaba da aikin gidanta da take gini a Abuja, ya ce mata ai bashi da kuɗi sai ta fusata sosai ta daina kiransa a waya.
“Ta yi tunanin bani da shi ne, ya sa ba na son kashe mata kuɗi da yawa kamar yadda nake yi a baya.
“Ta gaya min cewa ta sami sabon saurayi daga baya ta tura hotonta tare da sabon masoyin nata a WhatsApp dina, wanda hakan ya tunzura ni,” kamar yadda ɗan Chainan ya shaida wa kotu.