Tsohuwar ministar jin-ƙai, Sadiya Farouq, ta miƙa kanta ofishin EFCC

0
181

Tsohuwar ministar ayyuka da jin-ƙai ta Najeriya Sadiya Umar Farouq ta kai kanta a gaban hukumar EFCC a Abuja babban birnin Najeriya.

Ana zargin wani kwangila a ma’aikatarta da almundahanar sama da naira biliyan 37.

Tun a makon da ya gabata ne hukumar ta gayyaci tsohuwar ministar ta gabatar da kanta, sai dai wasu majiyoyi sun tabbatar da ba ta je ba.

A safiyar Litinin tsohuwar ministar ta fitar da sanarwa a shafinta na X inda ta sanar da zuwanta hukumar.

KU KUMA KARANTA: EFCC ta gayyaci tsohuwar ministar Buhari, Sadiya Farouk

“Bisa radin kaina, na isa hedikwatar hukumar da ke yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zango ƙasa (EFCC) domin karɓar goron gayyata domin ƙarin haske dangane da wasu lamura waɗanda hukumar ke bincike a kai,”

Sai dai a kwanakin baya, tsohuwar ministar ta wallafa wani saƙo a ranar 26 ga watan Disambar 2023 inda take nesanta kanta daga duk wasu rahotanni da ke nuna cewa EFCC na bincike a kanta inda hasalima ta yi zargin ana ƙoƙarin ɓata mata suna.

Leave a Reply