Tsohon Ɗan wasan Super Eagle ya zama sabon mataimaki mai horar da Club Brugge
Daga Jameel Lawan Yakasai
Joseph Akpala, tuni kungiyar ta sanar ya zama mataimakin mai horarwa Nicky Hayen a kungiyar ta Club Brugge ta kasar Belgium.
KU KUMA KARANTA: Gwamnan Kano ya bawa masarautu umarnin fara shirye-shiryen hawan bukin ƙaramar Sallah
Akpala, a baya ya bugawa Club Brugge wasa daga 2008-2012 inda ya zura kwallo 39, a wasa 105, kafin ya koma Werder Bremen ta kasar Jamus.
Haka zalika a baya ya bugawa Najeriya wasa tara kafin daga bisani ya sanar da murabus a matsayin dan wasa.









