Kamfani na ne ke biyan haraji mafi yawa a Najeriya – Dangote

0
51
Kamfani na ne ke biyan haraji mafi yawa a Najeriya - Dangote

Kamfani na ne ke biyan haraji mafi yawa a Najeriya – Dangote

Daga Jameel Lawan Yakasai

Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya shaida wa Shugaba Bola Tinubu cewa rukunin kamfanoninsa ya biya haraji har Naira biliyan 450 ga asusun Gwamnatin Tarayya a shekarar 2024, wanda hakan ya sanya shi zama kamfani mafi biyan haraji a Najeriya.

Da wannan babban adadin haraji da aka biya, kamfanonin Dangote sun fi dukkan bankunan Najeriya haduwa wajen biyan haraji.

Dangote ya bayyana cewa duk da biyan harajin Naira biliyan 450 a bara, Rukunin Kamfanin zai ci gaba da kashe karin Naira biliyan 900 wajen gina hanyoyin mota a fadin Najeriya.

Ya ce hanyar zuwa tashar jiragen ruwa mai zurfi (Deep-Sea Port Access Road) na daga cikin hanyoyi da kamfanin Dangote ke ginawa karkashin tsarin dawowar haraji (tax credit scheme) na Gwamnatin Tarayya.

KU KUMA KARANTA: Farashin man fetur ya ƙaru sakamakon hana Ɗangote mai a Naira

A cewar Dangote, hanyar zuwa tashar jiragen ruwa mai zurfi tana cikin manyan ayyukan hanyoyi guda takwas da ke da jimillar nisan kilomita 500, ciki har da guda biyu da ke Jihar Borno da za su hada Najeriya da kasashen Chadi da Kamaru.

Ya yabawa Shugaba Tinubu kan irin jagorancin sa, yana masa kallon jarumi wanda gwamnatinsa ta dawo da kwarin gwiwar masu zuba jari a bangaren masu zaman kansu.

Dangote ya kara da cewa an saka wa hanyar da ke kaiwa zuwa sabuwar matatar man fetur ta zamani da ke karkashin Kamfanin Dangote suna “Bola Ahmed Tinubu Road” domin girmama Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

“Yallabai, bari in bayyana abu daya babban hanyar da ke kaiwa cikin matatar man mu za a kira ta Bola Ahmed Tinubu Road.”

Leave a Reply