Tsare-tsaren shugaba Tinubu sun ceto fannin noma daga halin koma-baya – Minista Aliyu Sabi

0
144
Tsare-tsaren shugaba Tinubu sun ceto fannin noma daga halin koma-baya – Minista Aliyu Sabi

Tsare-tsaren shugaba Tinubu sun ceto fannin noma daga halin koma-baya – Minista Aliyu Sabi

Daga Shafaatu Dauda Kano

Ƙaramin Ministan Noma da Tsaron Abinci, Hon. Aliyu Sabi Abdullahi, ya bayyana cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na aiwatar da manyan tsare-tsare da suka farfado da fannin noma da samar da isasshen abinci a Najeriya. Ya bayyana hakan ne a taron tunawa da Sardaunan Sakkwato da aka gudanar a Kaduna, inda ya ce gwamnati ta gaji fannin noma cikin matsaloli amma yanzu ta fara warware su.

Ministan ya ce gwamnatin Tinubu ta magance matsalolin tsaro da suka hana manoma komawa gona, ta hanyar ayyana dokar ta-baci kan harkar abinci. Ya ce an raba kayan abinci da shinkafa ga jihohi, da kuma samar da takin zamani da magungunan feshi. Haka kuma, an kaddamar da shirin “Soil Health Care” da zai inganta ƙasar gona ya rage yawan kudin da ake kashewa wajen noma.

KU KUMA KARANTA: Farashin kayan abinci ya sauƙa sosai ,amma takin zamani ya fi ƙarfinmu – Manoma

Gwamnati ta inganta cibiyoyin bincike domin samar da iri masu jure cuta, wanda shine karon farko da aka ware kudade masu yawa tun bayan gwamnatin Shehu Shagari. Sama da manoma 107,000 sun amfana da shirin “Agro-Pocket” na noman alkama a hekta 123,000, inda Jihar Jigawa ta fi ko ina kokari.

Haka zalika, gwamnati ta dauki mataki kan cututtukan amfanin gona kamar Tomato Ebola da ginger blight. An raba taraktoci 2,000 da injinan noma 9,000, tare da aiwatar da shirin SAPZ domin sarrafa amfanin gona da samar da kasuwa ga manoma a jihohi.

A fannin kiwo da ruwa, an kammala dam-dam uku da za su yi ban ruwa a hekta 2,728, tare da kafa sabuwar Ma’aikatar Ci Gaban Kiwo da cibiyoyin kiwo da mayanka. Ya ƙara da cewa, Gwamnati na haɗin gwiwa da jami’o’i da kungiyoyin manoma domin inganta noma, kiwo da tabbatar da tsaron abinci a kasar.

Leave a Reply