Tinubu zai naɗa sabon shugaban EFCC watanni huɗu bayan dakatar da Abdulrasheed Bawa

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na shirin naɗa Olanipekun Olukoyede a matsayin babban shugaban hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa ta EFCC.

Alfijir Labarai ta rawaito Lauyan mai suna Olukoyede ya yi aiki a matsayin sakataren EFCC na tsawon shekaru biyu a ƙarƙashin tsohon shugaban riƙo Ibrahim Magu.

An dakatar da shi daga aiki tare da Magu a shekarar 2020 kuma ba a sake ƙiransa ba.

Kafin aikinsa na sakatare, Olukoyede shi ne shugaban ma’aikatan Magu.

Ana sa ran za a sanar da naɗin nasa, wanda ke buƙatar amincewar Majalisar Dattawa “nan ba da jimawa ba,” a cewar majiyoyin da ke da masaniya kan ci gaban.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *