Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarnin dawo da shirin Gwamnatin Tarayya na ciyar da ɗalibai a makarantu.
Tinubu ya dawo da shirin ciyar da ɗaliban ne da nufin rage yawan ƙananan yara marasa zuwa makaranta da suka gararamba a kan tituna.
Gwamnatin da ta gabace shi, ta tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ce ta dakatar da tsarin bayan shekaru da farawa.
Amma Tinubu ya ce dawo da tsarin zarin samar da mafita daga matsalar rashin zuwa makaranta a tsakanin yaran.
A cewarsa, muddin ba a magance matsalar da yaran suke fuskanta a wajen neman ilimi ba, magance matsalar rashin zuwa makarantar yara zai yi wuya.
KU KUMA KARANTA: Gwamna Buni ya nemi haɗin kan jami’o’in Burtaniya uku, don bunƙasa harkar ilimi a jihar Yobe
Ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamman, ne ya sanar da hakan a taron laluɓo hanyoyin samun nasara da a ma’aikatar ilimi daga 2023 zuwa 2027.
Ministan ya ce shugaban ƙasa ya ɗauke ciyarwan daga hannun ma’aikatar ayyukan agaji ya dawo da shi ƙarƙashin Ma’ikatar Ilimi.