Taron ƙungiyar AU na nemo hanyar warware matsalolin da ke addabar nahiyar Afirka

0
165

Shugabannin ƙasashen Afirka sun buɗe wani taro na kwanaki biyu a ranar Asabar, yayin da nahiyar ke kokawa da juyin mulki da rigingimu da rikicin siyasa da kuma zaman ɗar-ɗar a yankin.

Gabanin taron da za a yi a Addis Ababa babban birnin ƙasar Habasha, shugaban hukumar Tarayyar Afirka Moussa Faki Mahamat, ya yi tsokaci kan tashe-tashen hankula da ke addabar kasashe da dama, na Afirka da sauran sassan duniya.

Sudan na cikin “rikici,” in ji Faki, yayin da yake bayyana barazanar ‘yan ta’adda a Somaliya, da “rikicin marar ƙarewa” a gabashin Jamhuriyar Demokraɗiyyar Kongo, da “haɗarin ta’addanci” a yankin Sahel, da kuma rashin zaman lafiya a Libya.

“Sake dawo da juyin mulkin soji da tashin hankali kafin zaɓe da bayan zaɓe, da rikicin jin ƙai da ke da nasaba da yaƙi da ko kuma illar sauyin yanayi, duk wani abu ne mai matuƙar damuwa a gare mu,” kamar yadda ya shaida wa ministocin harkokin wajen Afirka a ranar Laraba.

An buɗe ƙaramin taron ƙolin da nufin lalubo hanyoyin sake ƙaddamar da shirin samar da zaman lafiya ga DR Congo ciki har da shugaban Congo da abokin hamayyarsa na Ruwanda, wanda aka buɗe ranar Juma’a a gefen manyan tarukan ƙungiyar AU, kuma zai ci gaba a ranar Asabar.

Sai dai an daɗe ana sukar ƙungiyar mai mambobi 55 da cewa ba ta da wani tasiri, kuma ba ta ɗauki ƙwararan matakai ba wajen fuskantar tashe-tashen hankula da ƙwace madafun iko.

KU KUMA KARANTA:Turkiyya na fatan bunƙasa kasuwanci da Saudiyya zuwa dala biliyan 30

Nina Wilen, daraktan shirin Afirka a cibiyar nazarin hulɗar ƙasa da ƙasa ta Egmont Royal da ke Brussels, ta ce “Ina shakkun cewa za a yanke hukunci mai ƙarfi.”

Ya zuwa yanzu dai ƙungiyar ta ƙasashen Afirka ba ta da wani tasiri sosai kan ƙasashen da suka fuskanci juyin mulkin baya-bayan nan, in ji ta, ta kuma ƙara da cewa ƙasashe mambobin ƙungiyar ba sa son kafa abubuwan da za su ci karo da muradunsu.

Daga cikin waɗanda suka halarta daga wajen yankin har da shugaban ƙasar Brazil Luiz Inacio Lula da Silva. Sai dai babban sakataren MDD Antonio Guterres bai halarci taron ba, yayin da mai magana da yawunsa Stephanie Tremblay ta shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP, cewa yana da matsalar jirgin sama kuma bai samu damar tashi zuwa Addis Ababa ba.

Leave a Reply