Takarar kujerar majalisar dattawa, za a dogara ne da kundin tsarin mulki – Yari

Zaɓaɓɓen Sanata, Abdulaziz Yari, ya ce takarar neman kujerar shugabancin majalisar dattawa ta 10 za ta dogara ne akan tanade-tanaden kundin tsarin mulki ba wai umarnin kowa ba.

Sanata Yari, wanda kuma shi ne tsohon Gwamnan Zamfara, ya bayyana haka ne a ranar Juma’a a lokacin da yake ganawa da shugabannin ƙungiyar Tinubu Shettima Network, (TSN), ƙarƙashin jagorancin shugabanta na ƙasa, Dakta Kailani Muhammad, a Abuja.

Yari dai ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin majalisar dattawa ta 10. Zaɓaɓɓen Sanatan ya bayyana takarar a matsayin sanatocin, wanda tsarin mulki ya goyi bayan zaɓen shugaba a cikin su.

KU KUMA KARANTA: Shugaban majalisar dattawa ya buƙaci jam’iyyun adawa su haɗa kai da gwamnati mai zuwa

“Shugaban majalisar dattawa sanatoci ne kuma a ranar ‘D- day’ da za mu zaɓi shugaban mu, za mu yi abin da ake buƙata. “Lokacin da muka yi haka, ba na kowa ba ne. Muna yin abin da tsarin mulki ya ce mu ɗauki shugabanmu a cikin kanmu.

“Wannan shi ne abin da sassan kundin tsarin mulkin ƙasar suka bayyana a fili. Abin da zai faru a wannan ranar,  zai faru ne bisa ga umarnin tsarin mulki ba na kowa ba.

“Don haka, za mu yi amfani da ‘yancinmu na tsarin mulki a can,” in ji Yari Ya yabawa TSN bisa goyon bayansa na zama shugaban majalisar dattawa na 10, yana mai cewa aikin da ƙungiyar ke yi a fannin neman goyon bayan manufarsa abin yabawa ne.

A cewarsa, wannan zama na musamman da muke da shi tare da shugabannin TSN. Idan za a iya tunawa makonni huɗu da suka gabata ina ofishinsu inda na bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin majalisar dattawa.

“Na zo ne don neman goyon bayansu kuma dukkan shugabannin hukumar sun ba da alƙawuran da za su ba ni goyon baya a wannan takara. “Kuma a yau, za mu sake duba abin da ya faru daga lokacin zuwa inda muke a yau.

“Daga abin da muke gani da kuma karɓa daga kafofin watsa labarai ya nuna a fili cewa aikin yana kan ci gaba kuma yana da kyau sosai. Don haka, ƙungiyar tana aiki sosai,” in ji Yari.

A nasa jawabin, Muhammad ya ce maƙasudin taron shi ne don yiwa Yari bayanin irin nisan da ƙungiyar ta yi ta fuskar wayar da kan jama’a, inda ya ce ta samu sama da kashi 70 cikin 100 na ayyukan.

Ya bayyana ƙwarin guiwar cewa zaɓaɓɓen sanatan da ya shiga majalisar dattawa ta shida da yardar Allah zai zama shugaban majalisar dattawa ta 10.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *